Bello Tūrji Ya Amince Al'ummar Moriki Su Biya Naira Miliyan 30 Maimakon Miliyan 50 Da Ya Fara Bukata A Matsayin Fansa
- Katsina City News
- 08 Sep, 2024
- 259
Zaharaddeen Ishaq Abubakar, Katsina Times. Satumba 8, 2024
Shahararren ɗan ta'addan nan, Bello Tūrji, ya amince al'ummar garin Moriki dake jihar Zamfara su biya naira miliyan 30 maimakon naira miliyan 50 da ya bukata a farko, a matsayin kuɗin Fansa. Wannan na zuwa ne bayan da sabon kwamandan sojojin yankin ya kashe masa dabbobi a wani hari da aka kai.
Tūrji, wanda aka san shi da tilasta biyan kudaden fansa ga mutane a yankunan da ke ƙarƙashin Ikon sa, ya tilasta wa al'ummar Moriki biyan wannan kuɗin. Rahotanni sun nuna cewa ya bai wa al'ummar wa'adin zuwa ranar Laraba domin su cika wannan buƙata. Wannan na zuwa ne bayan ya yi barazanar kai hari ga al'ummar idan basu biya ba.
A cewar wani kwararre kan sha'anin tsaro, Audu Bulama Bukarti, ya bayyana a shafin sa cewa, kowanne magidanci a Moriki ya kasance dole ne ya bayar da naira dubu 10, yayin da matasa da basu da aure za su biya naira dubu 2.
Wannan tsari na biyan kuɗin haraji ko Fansa, ya zo ne duk da yunƙurin da sabon kwamandan sojojin yankin ke yi na hana al'ummar garin bada waɗannan kuɗaɗen ga 'yan bindigar. Kwamandan ya yi kira ga al'ummar da su ki yarda su biya waɗannan kuɗaɗen, yana mai cewa ba za su amfana da yin haka ba.
Sai dai a cewar wasu mazauna garin, sun bayyana cewa suna cikin tsaka mai wuya. Akwai fargabar cewa, idan suka ki biyan kuɗin, 'yan bindigar za su iya kai hari mai muni wanda zai iya salwantar da rayuka da dukiyoyi. Wannan shi ne babban dalilin da ya sa wasu daga cikin mazauna garin suka yanke shawarar cewa ba su da wani zaɓi illa su biya kuɗin harajin don kare lafiyar su da iyalansu.
Illolin Biyan Haraji Ko Fansa Ga 'Yan Bindiga
Biyan kuɗin haraji ko fansa ga 'yan bindiga na da illoli masu tarin yawa, musamman ma ga rayuwar al'umma a yankunan da abin ya shafa. Da zarar an fara bada kuɗin haraji ko fansa, 'yan bindigar kan samu ƙarfin guiwa su ƙara tilastawa al'umma irin waɗannan kuɗaɗen, wanda ke ƙara musu ƙarfi da damar ci gaba da aikata miyagun laifuka.
Haka zalika, biyan waɗannan kuɗaɗen na ƙara wa 'yan bindiga damar samun makamai da kayan aiki da za su ci gaba da kai hari a wasu yankuna. Wannan na sa ci gaba da ta'addanci da rashin zaman lafiya a cikin al'umma.
A cewar masana harkar tsaro, ya kamata gwamnati da jami'an tsaro su ƙara ƙaimi wajen magance wannan matsala ta biyan kuɗin haraji ko fansa ga 'yan bindiga, ta hanyar kawo karshen ƙungiyoyin 'yan ta'adda da kuma kafa tsayayyen tsari na tsaro a yankunan da ake fama da matsalar.
Bukatar Gaggawa na Magance Matsalar
Don magance irin wannan lamarin, masana harkokin tsaro suna ganin akwai bukatar gwamnatin Najeriya da jami'an tsaro su ɗauki matakai na gaggawa domin kawo ƙarshen wannan muguwar al'ada ta biyan kuɗin haraji ga 'yan bindiga. Hakan zai taimaka wajen rage tasirin da 'yan bindigar ke yi a yankunan karkara da kuma samar da tsaro ga al'ummar da ke cikin wannan hali na rashin tabbas.
Gwamnati da hukumomin tsaro su ne kawai ke da alhakin kare rayuka da dukiyoyin al'umma, ba su ne za su tsaya jiran 'yan bindiga su karɓi haraji daga hannun talakawa ba. Tsarin biyan haraji ga 'yan bindiga yana nufin cusa tsoro a zukatan jama'a, wanda hakan na jawo koma baya wajen tabbatar da zaman lafiya da ci gaba a al'umma.
Bello Tūrji da 'yan tawagarsa suna ci gaba da kawo wa al'ummar Zamfara da makwabtan ta kalubale ta hanyar tilasta musu biyan haraji da barazana ga rayukan su. Duk da yunƙurin sojoji na kawo ƙarshen wannan ta'addancin, har yanzu akwai bukatar ɗaukar matakai na musammam don tabbatar da tsaron al'umma, ba tare da su tilasta biyan kuɗaɗe ga 'yan bindigar ba.