NNPC Ltd Ba Ita Ce Kaɗai Ke Siyan Kayayyaki Ba; Kasuwa A Bude Take Don Farashin Mai Rahusa Daga Kowace Masana'antar Fetur Ta Cikin Gida
- Katsina City News
- 07 Sep, 2024
- 302
SANARWAR MANEMA LABARU
Hankalin Kamfanin NNPC Ltd ya kai ga sanarwar da Kungiyar Kare Haƙƙin Musulmai ta Ƙasa (MURIC) ta fitar, wadda ta yi zargin cewa Kamfanin Dangote Refinery Limited (DRL) na fuskantar cikas daga ayyukan Kamfanin Man Fetur na Ƙasa (NNPC Ltd). MURIC ta bayyana cewa canje-canjen farashin mai na PMS kwanan nan zai hana Dangote Refinery siyar da mai a farashi mai rahusa, sannan kuma NNPC Ltd ce kaɗai ke siyan dukkan kayayyakin daga kamfanin.
Domin fayyace gaskiya, NNPC Ltd tana son bayyana waɗannan abubuwan kamar haka:
1. Farashin kayayyakin mai daga kowace masana'antar fetur, ciki har da Dangote Refinery Ltd (DRL), yana karkashin ikon yanayin kasuwar duniya. Canje-canjen farashin mai na PMS kwanan nan ba su da wani tasiri ga ikon DRL ko kowace masana'antar fetur ta cikin gida wajen shiga kasuwar Najeriya. A maimakon haka, idan farashin da ake sayarwa yanzu ana ganin yana da tsada, wannan yana ba DRL damar siyar da kayanta a farashi mai rahusa a kasuwar Najeriya.
2. Har ila yau, muna jaddada cewa babu tabbacin samun rahusa daga masana'antar cikin gida idan aka kwatanta da tsarin farashi na duniya, kamar yadda DRL ta tabbatar. NNPC Ltd za ta siyi PMS daga DRL ne kawai idan farashin kasuwa na PMS ya fi na matatun cikin gida tsada. DRL da kowace masana'antar cikin gida suna da 'yancin siyar da kayayyakinsu ga kowanne mai siye bisa tsarin 'wanda ya yarda ya siya', wanda wannan ne tsarin da ake amfani da shi yanzu a dukkan kayayyakin da aka cire musu tallafi. NNPC Ltd ba ta da niyyar zama mai rarraba kayayyaki ga kowace hukuma a wannan yanayi na kasuwa mai ‘yanci, don haka batun zama kaɗai mai siyan kayayyaki ba ya tasowa.
3. NNPC Ltd ba za ta iya lalata wani kasuwanci da take da hannun jarin biliyoyin daloli a cikinsa ba.
4. A matsayinta na ƙungiyar fafutuka mai neman adalci, ya kamata MURIC ta tabbatar da sahihancin bayanai kafin fitar da sanarwar da ba ta da tushe, wadda ke iya hura wutar tunzura talakawan Najeriya kan NNPC Ltd.
Olufemi Soneye
Jami'in Hulɗa da Jama'a na NNPC Ltd
Abuja
6 ga Satumba, 2024