DAUDA LAWAL A SHEKARA 59: MAI GIDANA WANDA BAI DA JIJI DA KAI
- Katsina City News
- 03 Sep, 2024
- 373
Daga Sulaiman Bala Idris
A wata ziyarar aiki da na yi a tsakiyar watan Agusta, direbana a Jihar Taraba ya shafe kusan fiye da rabin tafiyar zuwa masaukin mu yana magana a kan Gwamnan Zamfara, wanda kuma shi ne mai gidana. Direban ya ambaci cewa gwamnan shi ne mafi ƙarancin shekaru a cikin gwamnoni, mutum na musamman, wanda kuma kuma bai gajiya da aiki. Na tasa kunne ina saurare saboda mun saba jin irin waɗannan daɗaɗan maganganu game da Dauda Lawal.
A yau, 2 ga Satumba, 2024, mai gidana, wanda a kodayaushe ake yawan ganinsa a matsayin matashi, yana cika shekara 59 a duniya. Tun a makon da ya gabata nake ta zurfafa tunani kan abin da zan rubuta a matsayin karramawa ga Gwamna Dauda Lawal. A baya na yi rubutu da yawa a irin wannan rana, amma waɗanda na fi so a zuciyata fiye da kowanne su ne masu taken ‘Dauda Lawal: Mutuminmu, Burin Al'umma’ da ‘Dauda Lawal Ɗin Da Na Sani’.
A ranar 29 ga Mayu, 2023, wani sabon babi ya buɗe a rayuwarmu yayin da Dauda Lawal, mutumin da muka sani a matsayin mai zaman kansa, ya karɓi kujerar gwamnan jha. A yanzu ya ɗauki nauyin mulkin jihar da ke fama da matsalar ’yan bindiga, koma-baya a ɓangaren harkokin ilimi, kiwon lafiya, da walwalar ma’aikatan gwamnati, da dai sauran muhimman batutuwa.
Tsawon shekaru kafin 29 ga Mayu, 2023, Dauda Lawal ya kasance mai gidana - mutum ne da ya saba kiran kowane ma'aikacinsa 'ɗan uwana.' Babu wani muƙami a duniya da zai iya canja karamci da mutuntakar Dauda Lawal.
Duk da cewa ranar 2 ga watan Satumba ba ranar tattauna ɗimbin nasarorin da Gwamna Dauda Lawal ya samu ba ne a matsayin gwamnan Zamfara a cikin shekarar da ta gabata, domin an yi ta yaɗa su a kafafen yaɗa labarai.
Yau rana ce da ta ya fi dacewa a bayyana salon jagoranci da halayen Gwamna Lawal. Idan har kana da abubuwa da yawa da za ka bayyana, zai fi dacewa ka taƙaita, domin wasu bayanai na buƙatar littafi ne (ina aiki a kan hakan. Littafi ne da zai wayar da kan mutane da dama).
Mai gidana Dauda Lawal mai saurare ne. Yana da salon da Shugaban Amurka na 30, Calvin Coolidge, yake cewa, 'Duk nagartaccen mutum ya kasance mai saurare.'
Ga Margaret J. Wheatley, ta ce, saurare yana matsar da mu kusa da al'umma kuma yana taimaka mana mu zama cikakkun mutane, maau lafiya, kuma masu hankali. Rashin sauraro yana haifar da rarrabuwa, kuma rarrabuwa shi ne tushen duk wani wahala.
Mai gidana, Dauda Lawal, Allah Ya yi masa da kusan komai. Na sha ji yana faɗin cewa da a ce an ba shi damar tsara rayuwarsa, ba zai iya tsara ta da ɗimbin ni’imomin da Allah Ya yi masa ba.
Mai gidana shi ne shahararre Dauda, wanda ya kasance abin yabo a gari. Sau da yawa mutane sukan yi hasashen da bai daidai ba wajen auna dukiyarsa, bq Naira kaɗai ba, har da dalar Amurka. Mai kamala da kyan hali, Dauda Lawal a kullum yana fitowa tamkar matashi mai shekaru arba'in da haihuwa saboda ya san saka sutura, haƙƙun!
Ba kamar sauran mutane masu irin muƙamin sa ba, ya ba ya jijinda kai. Mai gida na, mai tawali’u ne, mai janyo mutane kusa da shi, karɓar al'umma. Yana ƙarfafa ma'aikatansa sosai don su faɗi ra'ayoyinsu. Yana shirya taruka na kai-tsaye tare da ƙananan jami'ai, masu tsaron ƙofa, direbobi, masu kula da tsirrai, da masu goge-goge don sauraron ra'ayoyinsu game da yanayin aiki da duk wata damuwa da suke da ita.
Kasancewar mai gidana Dauda Lawal mai sanin makamar aiki ne, ya san duk abin da ke gudanar a cikin gwamnatin sa. Kwamishinoni, masu ba da shawara, da sauran manyan jami'an tawagarsa suna taka tsantsan a cikin ayyukansu domin yana da masaniya a kan komai. Ƙofofinsa a buɗe suke, kuma ana iya samun wayarsa a koda yaushe (Ina tsammanin ma kusan kowa yana da lambar wayarsa). Gidan Dauda shi ne mafi sauƙin shiga idan aka kwatanta da gidajen wasu gwamnoni.
Dauda Lawal mai kyauta ne mai fara'a. Shi ya sa mutanen da suka fi shan wahala a gwamnatinsa su ne waɗanda ke fama da matsalar ‘Sadistic Personality Disorder’ (kaɗan ne ma, idan akwai). Akwai mutaben da a kullum su na cikin fushi da baƙin ciki saboda mai gidana Dauda Lawal, yana jin daɗin bayarwa, taimako, da sanya murmushi a fuskokin al'umma. Wani abu mai daɗi shi ne babu wanda zai iya tilasta masa ya yi abin da ba daidai ba (ma'ana, ba a masa abin da Bahaushe ke cewa 'Ba a mugun sarki sai dai mugun bafade'). Babu! Kar ka yarda wani ya yi maka ƙarya.
Idan kana son ka ɓata garrin ka a gaban Dauda Lawal, ka tunkare shi da tsegumi da ’yan ƙananan maganganu. Yana daraja ikhlasi kuma ba ya son fasiƙanci da rashi gaskiya. Yayan yawan cewa ba ya son aiki 'kiya'. Ƙwararre ne wanda ke da ƙwarawa sosai a harkokin sa.
A duk lokacin da na shafe tare da shi, na san cewa mai gidana yana saurin fushi da mutanen da ba su da tsafta. Yana son tsafta sosai kuma yakan jaddada muhimmancin goge haƙora da yin amfani da tuaren jiki na 'deodorants' da turaren kaya mai kamshi mai daɗi ba mai hawa kai ba. Bai zai yiwu a kusanci shi da warin baki ko warin jiki ba; abu ne da zai masa daɗi ba.
Yayin da ka ke cika shekaru 59 a daniya a yau, ina so ka sani cewa mutane da yawa su na sha'awar salon ka kuma suna girmama ka. Ka samu mutuntakar ka wajen ayyukan taimako a ɓangaren kamfanoni masu zaman kansu, kuma yanzu ka kafa tarihi a matsayinka na jagoran tawagar ceto Zamfara. Barka da Ranar Haihuwarka, Gamjin Zamfara!
Sulaiman Bala Idris shi ne Mai Magana da Yawun Gwamnan Jihar Zamfara.