Friday : January 10, 2025
04 : 13 : 02 AM

Tsohon Mataimakin Gwamnan Jihar Katsina Ya Sauya Sheƙa Daga Jami'ayyar PDP Zuwa Jam'iyyar APC

top-news



Ranar Lahadi 1 ga watan Satumba 2024, Jam'iyyar APCn jihar Katsina tayi babban kamu, inda tsohon mataimakin Gwamnan jihar, ya sauya sheƙa daga Jami'ayyar adawa ta PDP zuwa jam'iyya mai mulki ta APC.

Tsohon mataimakin Gwamnan Hon. Surajo Umar Damari, wanda yayi ma tsohon Gwamnan Jihar Katsina Barr. Ibrahim Shehu Shema mataimaki a wa'adin mulkin shi na farko, Ya amshi katin shedar zama ɗan jam'iyyar APC bayan ficewa daga jam'iyyar PDP. 

A lokacin da ya bashi takardar shedar zama ɗan jam'iyyar APC a wajen taron jin ra'ayoyin al'umma da Gwamnan Jihar Katsina Malam Dikko Umaru Radda Ph.D ya yi a shiyyar Funtua Mataimakin Shugaban Jam'iyyar  Hon. Bala Abu Musawa 

Tun farkon Jawabinsa a wurin taron ya fara da ba yan jam'iyyar adawa da kuma iyayen ƙasa haƙuri akan shiga al'amurran siyasa da yayi, duk da ba shine abinda ya tara al'umma a wajen ba, ya kara da cewa, amatsayinmu na yan siyasa duk inda mukaga kofa sai munyita koda kadance.