An Maida Matsalar Rashin Tsaro Wani Makamin Da Ake Amfani Da Shi Domin Cimma Muradun Siyasa -Ngozi
- Katsina City News
- 26 Aug, 2024
- 326
Najeriya...Tsohuwar Ministan Kuɗin Najeriya Okonjo-Iweala....
Ngozi Okonjo-Iweala, wadda itace babbar darakta Cibiyar Kasuwanci ta Duniya wato World Trade Organisation (WTO), tace saboda wasu dalilai na siyasa an maida matsalar rashin tsaro ta zama wani makamin da ake amfani dashi domin cimma Muradun Siyasa.
Okonjo-Iweala ta furta haka ne a ranar Lahadin da ta gabata yayin da ake buɗe taron ƙarawa juna sani na ƙungiyar lauyoyin ta Najeriya a birnin Lagos wato 2024 Annual General Conference of the Nigerian Bar Association (NBA).
Tace babu wani ci gaba da zai iya samuwa matsawar dai babu cikakken tsaro a ƙasa.
“Babu ta yadda zamu iya samun abubuwan more rayuwa matsawar babu tsaro,” a cewar ta.
“Ba zamu taɓa samun tsaro ba da za'a ce ba za'a samu ci gaba ba, mu duka mun sani cewa an maida matsalar rashin tsaro wani makamin siyasa da ƴan siyasa suke amfani dashi a ƙasar nan, wanda kawo yanzu shine ya tsunduma mu a halin da muke ciki.
“Muna da ƴan siyasa waɗanda suke ganin cewa hanya mafi sauƙi da zaka nuna Abokin adawar ka bai iya mulki ko jagoranci ba shine ta hanyar amfani da matsalar rashin tsaro ba tare da damuwa ko laakari da mi hakan ka iya jawowa ba na rasa rayukan Al'umma da asarar dukiyoyin waɗanda basuji ba basu gani ba, ya zama wajibi a dakatar da irin wannan tunanin.
Okonjo-Iweala tace yawan satar Ɗanyen man fetur da akeyi a Najeriya ya durkusar da tattalin arzikin ƙasar.
“Shekara da Shekaru ƴan Najeriya sun ga yadda ake haɗin guiwa ana Sace gurbataccen man fetur a ƙasar nan Lamarin da ya durkusar da tattalin arziki ƙasar baki ɗaya a cewar ta.
“Ya kamata duk ƴan Najeriya su yadda cewa satar duk wani arzikin ƙasar nan koma minene zunubi ne babba kuma dole a haɗa ƙarfi da ƙarfe a dakatar da faruwar hakan .”
Tsohuwar ministan tace akwai fasahohin zamani da dama da ya kamata ayi amfani dasu wajen ganowa tare da dakatar da masu yunƙurin satar man a Najeriya, babu wani excuse da wani zai bada akan wannan.