Gwamna Radda ya Raba Shinkafa Buhu 4,019 ga Mabuƙata a Ƙaramar Hukumar Katsina
- Katsina City News
- 07 Sep, 2023
- 798
Zaharaddeen Ishaq Abubakar, Katsina Times 7/9/2023
Gwamnan jihar Katsina Malam Dikko Umar Radda a ranar Alhamis 7 ga watan Fabrairu Gwamnan Radda ya raba Tallafin Shinkafa ga Mata Zawarawa, Tsaffi, da Masu Buƙata ta Musamman don rage Raɗaɗin rayuwa.
Gwamnan ya bayyana a filin wasa na Muhammadu Dikko dake cikin garin Katsina inda ya Dunga tantancewa da kansa, kuma yana sanya Ido da kwato wasu da suka yi yunkurin karkatar da tallafin.
Tallafin da mafiya yawa da suka ci gajiyarsa Mata ne da tsaffi, kuma sun samu kudin cefane naira dubu goma-goma.
Kamar yanda Gwamnan ya sanar yace, "ba a karamar hukumar Katsina kawai zamu raba wannan Tallafin ba, zamu raba dukkanin kananan hukumomi guda 34 na jihar Katsina, kuma mun sanya an tantance an gano mana Mabuƙata na hakika wadanda ko wannensu zamu bawa buhun shinkafa da naira dubu goma."
Gwamnan ya kuma ce shi wannan tallafin baya cikin wancan tsarin na Ƙananan hukumomi da suka raba masara, da kuma na Gwamnatin tarayya da ta bawa jihar rancen naira biliyan biyu don sayen kayan abinci da tallafawa Mabuƙata na rage Raɗaɗin cire tallafin manfetur.
Radda ya ce Tallafin zai cigaba a duk lokacin da dama ta samu kuma bisa adalci da gaskiya kamar yanda suka dauki alkawari.