Ranar Harshen Hausa ta Duniya! 26/8/2024
- Katsina City News
- 26 Aug, 2024
- 256
Maulana (Dr) Sheikh Muhammad Nasir Kabara ya ba da gudummawa gagaruma wajen haɓaka harshen Hausa da bunƙasa shi a Nigeria da Africa dama duniya baki ɗaya.
Ya yi amfani da Harshen Hausa wajen koyar da Sunna ta Shugaba ( sallal Lahu alaihi wa alihi wassalam.) da kuma yaɗa aƙidar Ash'ariyyah, da mazhabar Malikiyah da kuma koyar da sufanci duk a cikin Harshen Hausa don iyar da saķo ga al'ummar Hausawa da ma su jin harshen Hausa a ko ina su ke.
A cikin gudummawar da Maulana Ameerul Jaishi ya bayar wajen yaɗa ilimin addini da fannoni dabam dabam tun daga kan Tauhidi, Hadith, Fiqhu, Sirah, Sufanci.. da sauran su. Bai tsaya nan ba sai da ya fassara wasu daga mafiya muhimmancin littatafan Musulumci zuwa harshen Hausa don kusanto da fahimtar addini ga al'umma.
Daga muhimman aikace aikacen sa da rubuce rubucen sa da su ka taimaka wajen bunƙasa harshen Hausa da inganta shi sun haɗa da:-
1) Shi ne ya fara fassara Alƙur'ani zuwa Harshen Hausa a cikin mujjaladai 3, ya sa wa Tafsirin sunan " IHSANUL MANNAN".
Ya yi haka ne don kusanto da ma'anonin Al-Qur'ani Mai Girma ga masu magana da harshen Hausa. Wannan tafsiri ya ba da babbar gudummawa wajen bunƙasa harshen Hausa.
2) Maulana (Dr.) Sheikh Nasir Kabara ya fassara babban littafin nan da ya ke koyar da ƙaunar Shugaba sallal Lahu alaihi wa alihi wasallam, da sanar da haƙƙoƙin sa, na Shaikh Al-qadi Iyad, "KITABUSH SHIFA FIT TA'ARIFI Bi HUQUQIL MUSƊAFA".
Shi ma wannan littafi Maulana Ameerul Jaishi ne farkon wanda ya fassara shi zuwa Harshen Hausa don koyar da ƙaunar Shugaba (sallal Lahu alaihi wa alihi wassalam) a zukatan al'ummar Hausawa. Ya sanya ma sa suna: "MARMARO GARAI GARAI MAI TACECCEN BAYANONIN ASSHIFA KWARAI KWARAI".
Wani muhimmin al'amari da ya kamata manazrta da ma su binciken harshen Hausa su ba shi kulawa ta musamman, shi ne waďannan littatafai biyu, wato Tafsirin Al-Qur'ani da ya rubuta cikin Hausa da fassarar sa ga littafin Asshifa.
Babu shakka waďannan lattattafai biyu wata taska ce mai tsadar gaske wadda ta ke maķil da kalmomin Hausa na asali, ko mu ce tsohuwar Hausa, wadda malam yai matuķar ķoķari ya tsefe ya tace, don tsare wa Hausawa harshen su na ainihi.
3) Ya na da rubuce rubuce ma su tarin yawa na waƙoƙi da ya tsara cikin harshen Hausa da kuma zube, don koyar da iliman Musulumci kamar: Tauhidi, da Fiqhu, da Sufanci.. da sauran su.
Daga cikin su akwai fassara "Manzuma ta Qurďubiy" zuwa harshen Hausa, wacce ta ƙunshi taceccen Fiqhun ibada a mazhabar Malikiyyah.
Ya yi wannan fassara a waķe, ya kira ta da "KAMALUL ILAHI".
Haka na akwai waƙar sa da ya kira ta "SHIRIYA TA RAHMANU", wadda ta ķunshi taceccen bayanin addini, wato Shari'a da Sufanci.
Haka shahararriyar waķar sa da ya kira ta da "JALALULLAHI", wadda ta ķunshi tsagwaron wa'azi.
Ya kuma yi tarin waķoķi na yabon Shugaba sallalLahu alaihi wa alihi wasallam da yabon manyan waliyan Allah.
Haka ba za mu manta da taceccen tarihin iyayen sa da kakannin sa da yai a waķe ba cikin harshen Hausa, wanda a ka fi sani da "Waķar Aya Shaihu Faruqu".. da sauran su.
4) Majlisan karatukan sa, musamman na Tafsir da Asshifa mabubbuga ce da al'umma ta saurari lafiyaiyar Hausa ta asali.
5) Bugu da ķari Malam Kabara teku ce mara gefe wajen sanin tarihin ķasar Hausa da asalin Hausawa, da zuzzurfan sanin sirri da dokokin harshen Hausa zuben sa da waķar sa.
A taķaice, Malam ya yi rubuce rubuce da aikace aikace da dama a harshen Hausa, wadanda su ka ba da babbar gudummawa wajen haɓaka harshen Hausa da inganta shi.
Allah ta'ala ya ƙara wa Maulana Ameerul Jaishi yardar sa, ya
sabunta rahama gare shi, ya nunnunka ladan sa, ya ba mu albarkar sa.
Wanda ya rubuta maƙala Sheikh Sidi Musal Qasiyuni Kabara
Mai yaɗawa Aminu Magaji Kabara.