Tatsuniya Ta 45: Labarin Wani Mutum Da 'Yarsa

top-news


Ga ta nan, ga ta nanku.

Wata rana wani mutum da ke garin Yamutsawa ya je gidan Sarkin garin. Ya ce yana so zai ba Sarkin 'yarsa ya aura. Shi kuwa Sarkin Yamutsawa ya dade da matansa biyu. Da Sarki ya ji haka, sai ya sanar da shi cewa ba zai kara aure ba. Ya ce idan ma ya auri mace ta uku, to kuwa zai gille mata kai. Sai mutumin ya ce: "Na ji, na yarda, ka aure ta ko za ka gille mata kai."

Shi kuma mutumin da man malami ne, ɗan baiwa. Shi ke nan, Sarki ya aure ta. Kamar yadda Sarki ya fada, washe-garin ranar da amarya ta yi kwanan farko a gidansa, sai ya sa aka fille mata kai. Amma kuma kullum idan an fille kanta, jim kadan sai ga wani kan ya fito.

Ana nan, sai matan Sarki biyu suka sami ciki, amma ita ba ta samu ba. Ganin haka, sai uban amarya ya sauya mata kama ya umarce ta da ta bi Sarki lokacin da zai fita farauta. Sai ko ta sami juna biyu a wannan lokaci. Bayan 'yan watanni ciki ya fito, Sarki ya tambaye ta: “A ina kika sami ciki?" Ba ta tsaya wata inda-inda ba sai kawai ta ce: "Kai ne ka yi min."

Shi kuma ya musanta. Amma sai ta yi masa bayani dalla-dalla cewa ai ta sauya kama ne sanda suka hadu, lokacin da ya je farauta. Da Sarki ya ji haka sai ya ce: *Ai mai wadancan kamannin da kika fada ta fi ki kyau." Da ta kara yi masa bayani, sai ya amince lallai shi ne mai cikin.

Bayan wani dan lokaci kuma, sai Sarki ya tara matan nan su uku ya ce: "Kowacce ta je ta haihu a gidansu." Sai kowaccensu ta kwashe kayanta, ta tafi gidansu. Ba da dadewa ba kuwa sai daya daga cikinsu ta haifi Bera, dayar kuma ta haifi yaro Kadangare, ita kuma amarya 'yar malami, ta haifi da kuma ya yi kama da ubansa, watau Sarki.

Da man ita wadda ta haifi Bera ta haihu ne a cikin toka, wadda ta haifi Kadangare kuma ta haihu ne a daji. Ita kuma 'yar malami, ta haihu ne a gidan ubanta, shi ya sa ta haifi mutum. Bayan sun gama wanka, kowacce ta koma dakinta, watau gidan Sarki.

Bayan 'yan kwanaki da komawar matan Sarki, sai ya ki kulawa da yaron da 'yar malam ta haifa domin shi har yanzu bai yarda da cewa ita ce ta haifi yaron nan ba. Sai ya yanke shawarar cewa a kai yaron reno gidan danginsa, kuma kada daya daga cikin matan ta sake ganin sa har sai ya girma sai a kawo shi ya nuna uwarsa da kansa.

A kwana a tashi, yaro ya girma, sai Sarki ya sa aka tara mutanen garin domin su ga abin da zai faru. Ya sa matansa su uku suka fito, ya tura su da dan. Yaro ya zo a kan Doki. Manufar taron dai ita ce yaron ya fid da wadda ta haife shi daga cikin matan Sarki. Sai kawai aka ji ya kama wannan waka:

"Wace ce uwata?
Tambaya nake,
Wace ce gyatumata?
Wace ce iyata, WO-Wo.
Ina kara tambaya,
Wace ce mahaifiyata?"

Sai matar Sarki wadda ta haihu a daji ta karbi waka:

"Ga ni, ga ni, ni ce, dana,
Ga ni, ni ce mahaifiyarka,
Ya kai dana.
Ga ni, ni ce gyatumarka, w0-Wo,
Zo in rungume ka,
Ya kai dana."

Da yaron ya ji bayanin da ta yi masa a cikin wakar, kuma bai gamsu ba, sai ya rera wata wakar yana cewa:

"A'a, a ina kika haife ni?
Gaya mini, a ina kika haife ni?
A ina kika haife ni, wo-wo?"

Da mutanen gari da Sarki sai duk suka yi shiru, suna jira su ji abin da za ta ce, ko zai tabbatar ita ce uwarsa, ko kuma ba haka ba ne.

Dai ta kashe murya wadda ta fi ta da zaki tana cewa:

"Ai a daji na haife ka,
A Dajin Karangiya na haife ka.
Kai Yarima,

Aia daji na haife ka,
Nia daji na haife ka, wo-wo."

Ba tare da wani bata lokaci ba, sai kawai ya ce:

"Je ki gaba,
Ki yi gaba,
Ba ke ce mahaifiyata ba.
Je gaba,
Ba ke ce mahaifiyata ba
Wo-wo,
Ba ke ce mahaifiyata ba."

Haka ta Rare, ta wuce tana jin haushi. Wadda ta haihu a toka ma ta zo, ita ma ya ce ba ita ce uwarsa ba. Da aka zo kan mahaifiyarsa, wadda ita ce ta karshe da ta fadi inda ta haife shi, sai ya yi wani gwauron tsalle don murna har sai da ya shallake rimin da ke kusa da fada. Jama'a ma suka barke da sowa, sai dan Sarki ya je ya rungume uwarsa don murna. 

Shi kuma Sarki saboda jin haushin matansa sun yi masa karya dangane da haihuwar magajinsa, sai ya sa aka fiffille musu kawuna. Ya sa aka raba kasarsa biyu. Shi ya ci gaba da mulkin rabi daga fadarsa, daya rabin kuma ya mallaka wa dan.

Malamin nan kuma uban matar Sarki ya riga ya tsufa. Jikansa dan Sarki kuma ya gina masa gida a bangaren kasar da uban ya mallaka masa. Labarin wannan abin mamaki ya wuce garin Yamutsawa domin ya gama ko'ina a garuruwan da suke kusa da shi.

Kurunkus

Abubuwan Da Labarin Yake Koyarwa

- Wajibi ne shugaba ya yi kyakkyawan bincike kafin ya zartar da kowane hukunci don ya kauce wa yin kuskure.
- Son zuciya yana haifar da bacin zuciya.

Mun dauko Labarin daga Littafin Taskar Tatsuniyoyi Na Dakta Bukar Usman

NNPC Advert