RAHOTON KASUWANCIN HUKUMAR NNPC TA SHEKARAR 2023.
- Katsina City News
- 24 Aug, 2024
- 179
... Ta samu ribar naira tiriliyan uku da Miliyan dari uku.
....Ta saka hannun jari na tarilyan biyu da dubu dari
....zata samar da danyen mai ganga Milyan biyu zuwa karshen shekarar 2024.
Fassarar Hassan M Tukur
@ Katsina Times
Kamfanin NNPC limited ya fitar da rahoton kididdigewar matsayin cinikayya ta shekarar kudi ta 2023 inda ya bayyanar da Samar da riba ta Triliyon ukku da milyan dari biyu da chasa'in da bakwai a karshen shekarar, Wanda ya nuna qarin Naira milyan dubu dari bakwai (700billion) watau kashi 28 bisa dari in aka hada da ribar shekarar 2022 Wanda Naira Triliyon tsayin cinikayya ta kamfanin ya nuna yadda ake tafiyar da al'amurra na kamfanin ba boye-boye.
"Matsayarmu ta yadda cinikayyar kamfanin ya nuna qwarewa duk qalubalen yadda hanyoyin gudanarwa da tattalin arziki na qasa yake, mun iya inganta Samar da kayayyakin mu da kudaden kamfanin Mai Girma da albarka"Ajiya ya fada.
Ajiya ya ma ce Samar da gaggarumar riba ya nuna tabbacin NNPC na cigaba da bunqasa don Samar da makamashi kamar yadda dokar sayar da man petur da dangoginsa watau(Petroleum Industry Act-PIA 2021) ta tanada Kuma bisa tsammanin masu ruwa da tsaki na kamfanin.
Ya yi bayanin cewa NNPC zata bayyana yadda za a saida hannun jari a bana bayan masu ruwa da tsaki da masu hannun jarin na yanzun sun yi taronsu.
Ajiya ya qaryata zancen da ake na biyan kudaden tallafin mai inda ya ce kamfanin kawai yana kula da gibin da aka samu ne wajen shigo da kayayyaki na man petur daga qetare.
Tun farko da yake jawabinsa, shugaban Hukumar gudanarwa na kamfanin NNPC, Chief Pius Akinyelure yace wannan kyakkyawan sakamako ya samu ne bayan Samar da dokar sayar da man petur da dangoginsa watau Petroleum Industry Act-PIA a shekarar 2021, kokarin Hukumar gudanarwa da haziqan ma'aikatan kamfanin.
Akinyelure ya qara da cewa masu ruwa da tsaki na kamfanin sun aminche da hannun jari na Naira Triliyon biyu da dari (2.1trn) don yayi dadaito da dokar sayar da man petur da dangoginsa watau Petroleum Industry Act-PIA 2021.
A nata jawabin wajen taron manema labarai, Mataimakiyar shugaban kamfanin, Mrs Oritsemeyiwa Eyusan tace da inganci da aka samu saboda sabbin jini da aka Samar wajen fada da barayin danyan man petur da kare bututai na man daga masu fasa su, NNPC zata cinma gurin Samar gangar man petur milyan biyu a rana a karshen shekarar nan.
Dangane da dogayen layukan motoci a Gidajen Man petur da ke IKKO da ABUJA, Mataimakin shugaban kamfanin na biyu, Mr Dapo Segun ya nemi 'Yan Najeriya da su nuna fahimta, inda ya ce kamfanin NNPC na aiki da sauran masu ruwa da tsaki domin inganta rarraba Man petur da dangoginsa.
Idan za a iya tunawa a shekarar 2021, NNPC ta fara bayyanar da riba a cinikayyar ta daga fadawa ta Naira bilyan 803 a 2018.
Ta sake rage faduwar a 2019 ta koma 1.9 bilyan naira.
Sai dai a 2020, ta bayyanar da riba ta 287 bilyan naira a yayin da a shekarar 2021 ta bayyanar da riba ta 674.1 bilyan naira.
Ribar 3.297 trillion itace ta fi kowace shekarar yawa tun da aka kafa kamfanin shekaru 46 da suka wuce.
Olufemi Soneye
Chief Corporate Communications