Gwamnatin Jihar Katsina da Kwamitin Jinƙai Na IRC Sun Ƙarfafa Haɗin Kai Don Ci Gaban Al’umma
- Katsina City News
- 20 Aug, 2024
- 314
Zaharaddeen Ishaq Abubakar, Katsina Times
Kwamitin Tallafin Jinƙai na Duniya International Rescue Comitee (IRC) ta sake tabbatar da sadaukarwarta ga ayyukan jinƙai a Jihar Katsina yayin wata ziyara da ta kai ga jami'an gwamnatin jiha. Taron, wanda aka gudanar a Ofishin Sakataren Gwamnatin Jiha, ya mayar da hankali kan ayyukan da ke gudana da kuma haɗin kai wanda zai inganta rayuwar al’ummar da ke cikin mawuyacin hali a wannan yankin.
Ruqayya Jibril, Ko’odinetan Hukumar Tallafin Jinƙai ta IRC, ta yi bayani kan manufar ziyararta, wadda ta ƙunshi ƙarfafa dangantaka da Gwamnatin Jihar Katsina da kuma sanar da jami’an gwamnati game da ayyukan da ke gudana da kuma waɗanda aka tsara. Jibril ta nuna godiyarta, goyon baya da haɗin kan da ta samu daga gwamnatin jihar, tana mai yaba wa dangantakar ƙwarai da aka kafa tare da wasu hukumomin jihar.
IRC, ɗaya daga cikin manyan ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa na ba da tallafi a duniya, ta fara ayyukanta a Najeriya tun a shekarar 2012, inda ta fara da wasu ayyukan jinkai kuma na gaggawa a jihohin Kogi, Adamawa, Borno, da Yobe. Hukumar ta faɗaɗa ayyukanta zuwa Arewa maso Yamma a shekarar 2021, bayan wasu matsalolin da suka taso na bukatuwar agajin gaggawa a yankin.
A Katsina, ayyukan IRC sun fi mai da hankali ne kan kiwon lafiya, abinci mai gina jiki, ruwa, tsaftar muhalli, da kuma kare hakkin al’umma. Hukumar na aiki tare da Ma’aikatar Lafiya, Hukumar Kula da Lafiya a Matakin Farko ta Jiha, da sauran hukumomin cikin gida don tallafawa da inganta tsare-tsaren da ake da su, tare da tabbatar da samar da ingantattun ayyukan kiwon lafiya. Wannan ya haɗa da samar da kayayyakin likitanci, horas da ma’aikatan lafiya, da kuma tallafawa shirye-shiryen kiwon lafiyar mata masu juna biyu da abinci mai gina jiki.
Jibril ta kuma yi bayani kan yadda IRC ke taimakawa wajen magance matsalar rashin abinci mai gina jiki tsakanin yara ‘yan ƙasa da shekaru biyar, tare da tallafawa kulawar al’umma wajen magance rashin gina jikin, da kuma haɗin gwiwa da UNICEF don samar da abinci mai gina jiki. Bugu da ƙari, IRC ta kasance tana taka muhimmiyar rawa wajen inganta ruwan sha da tsaftar muhalli a al’ummomi, musamman a Dandogoro, inda suka gyara rijiyoyin burtsatse tare da haɗin gwiwar Ruwasa da Ma’aikatar Albarkatun Ruwa.
IRC ta kuma taka muhimmiyar rawa wajen kare hakkin al’umma, inda take aiki tare da Ma’aikatar Harkokin Mata da Ilimin Yara Mata don samar da kulawa da kayan ɗaukaka martaba ga waɗanda suka tsira daga cin zarafi. Sashen farfaɗowar tattalin arzikin hukumar yana tallafawa hanyoyin samun abin rayuwa da noma, tare da samar da kuɗaɗen tallafi ga mutanen da rikici ya raba da muhallansu a jihohin Katsina, Zamfara, da Sakkwato.
A madadin Sakataren Gwamnatin Jihar Katsina, Alh. Salisu Abdu, Babban Sakataren Majalisar Zartarwa da Tsaro, ya yaba wa IRC kan gudunmawar da take bayarwa mai ma’ana a jihar. Ya nuna godiyar gwamnatin jiha ga ƙoƙarin da IRC ke yi a fannoni da dama, inda ya kwatanta ƙungiyar da “ƙaramar gwamnati” saboda yawan shiga ayyuka masu muhimmanci.
Alh. Abdu ya tabbatar wa IRC da ci gaba da haɗin kai da goyon bayan gwamnatin jihar, tare da jaddada mahimmancin irin waɗannan haɗin kan wajen cigaban jihar. Ya mika godiyar gwamnatin tare da yin addu’ar samun nasara ga ayyukan IRC, tare da tabbatar da cewa jihar ta shirya kuma tana da niyyar yin aiki tare da ƙungiyar don amfanin al’ummarta.
Taron ya jaddada dangantaka mai karfi tsakanin Gwamnatin Jihar Katsina da Hukumar Tallafin Jinƙai ta IRC, inda aka nuna sadaukarwa ta bai daya wajen inganta rayuwar al’ummomin da ke cikin mawuyacin hali a wannan yankin.