RUBZAWAR WANI BANGAREN GADAR KOFAR KWAYA. ...Gwamnati ta dauki matakin gaggawa
- Katsina City News
- 19 Aug, 2024
- 331
@ Katsina Times
Kamar yadda jaridun Katsina times suka bada labarin rubzawar wani bangaren gadar Kofar kwaya a ranar jumma ar data gabata.
Yanzu dai gwamnatin Katsina ta dauki matakin gaggawa,daga ranar jumma a zuwa jiya lahadi manyan jami an gwamnati daban daban suka je ganin me ya faru.
A jiya lahadi, an kuble hanyar da gadar ta samu matsalar an saka manyan makarai na sumunti.An kuma gano wani bangaren dake saman gadar da ya fara tara ruwa yana kwantawa, har ya fara lotsawa. shima an sanya masa alamar kar a bi ta saman shi.
A yau litinin ana ruwa wasu jami an gwamnati sun kara zuwa wajen gadar.binciken Katsina Times ya gano ba wani kudin da gwamnati zata sake kashewa, yan kwangilar sune zasu zo suga, ina sukayi kuskure har aka samu wannan matsalar su gyara aikin su da kansu.
@ Katsina Times