Sana'ar Tandun Man Shanu: Mutum Ɗaya Ya Rage a Katsina.
- Katsina City News
- 17 Aug, 2023
- 1096
Ko Wace Ƙabila tana da Sana'o,in da ta Dogara dasu, kuma take taƙama da Alfahari da ita. Kamar Hausawa, ansansu da Nau'ikan Sana'o,i Iri daban-daban, kama daga Sana'ar Ƙira, Saƙa, Wanzanci, Jima, Runi Dukanci Noma, da Sauransu. Haka zalika a cikin wadannan Sana'u na Hausawa ko wanensu yanada Reshe ko bangare, Misali Maƙera akwai, Maƙeran Farfaru, Akwai Maƙeran Babbaƙu, (Farfaru suna masu Sarrafa farin Ƙarfe irinsu Azurfa da Dangoginsu, inda Babbaku kuma suke ƙera Baƙin Karfe) haka sauran sana'o,in ko wanne da yanda rabe-rabensa kamar yanda Dukawa suma suka rabu gida-gida wato kowa da inda ya Ɗauka, kuma yafi Kwarewa.
So dayawa kuma ta hanyar wadannan Sana'un ake gane Basira ko Baiwar da Allah ya zuba a ƙwaƙwalwa da zuciyar Dan'adam.
Katsina Times tayi wani Dogon Bincike da Nazari kuma tana cikin yi, akan sana'o,in Malam Bahaushe da kuma irin Tasirinsu ga cigaban Tattalin Arziki.
Wanda kuma lokaci bayan lokaci zamu dunga tsakuro maku su da tattaunawa da masu yin irin sana'ar da kuma tasiri ko cigaba da sana'ar ta Malam Baushe take kawowa, kamar yanda muka Tattauna da Wani Bawon Allah da Malam Lawal na Inna, Baduku, amma ba na Ɗinkin Fata ba na Sarrafa fatar zuwa yin Abin Amfani Irinsu Tandun Kwalli da Tandun Manshanu, wanda kuma ahalin yanzu a cikin garin Katsina shi kaɗai ya rage a cikin masu irin wannan sana'ar.
Malam Lawal Na'inna Mai Tandu, ya shedawa Jaridar Katsina Times cewa har yau har gobe yana sana'ar Tandun Manshanu da ake yi da Fata, wanda a Zamanin Da, har a Birane ana amfani dashi, don kuwa yana daya daga cikin abinda ake hadawa Amare gara, don kuwa ana zuba manshanu a ciki a kaiwa Amarya.
Na'inna ya bayyana mana cewa yanzu idan yayi Tandun saidai yakai Kauye saboda su har yau har gobe basu yada al'ada ba don kuwa ana sayensa a can, amma a nan cikin birnin Katsina wani ma baisan sunansa ba, hakan kuma yana da alaka da ko in kula da Gwamnati, da sauran al'umma suke da sana'o,in gargajiya.
Yace shima ya gajeta ne ga mahaifinsa, mahaifinsa kuma ya mutu, yace ko a wancan lokacin a saninsa daga Katsina sai Karamar hukumar Kusada nan kadai ake wannan sana'ar ta yin Tandun Manshanu. Abinda bai sani ba a yanzu ko Kusada ana yinta Oho. Yace amma dai shi har yanzu yana yi kuma yana kaiwa kauyuka, saidai kuma Mafiya yawa anfi sayansa da Kaka lokacin ake cinikayya sosai.
Na'inna yace sana'ace mai rufin Asiri sosai don kuwa shi yaga haka, sana kuma sana'ace mai nuna tsantsan hikimar Bahaushe amma an watsar da ita, a halin yanzu duk Katsina shi kadai ne ke yinta, kuma duk ranar da babu shi shikenan sana'ar ta mutu. Ya bayyana.
Lawal Na'inna yaja hankalin Gwamnatin jihar Katsina da ta farfaɗo da ire-iren waɗannan sana'o,in ko don raya Al'adun Hausawa. Sana ya bayyana abinda yake fama da shi na karancin Jari wanda yace da yanada jari da Matasanmu basu mance da Tandun Manshanu ba. Kuma da ya inganta sana'ar tasa ta gado.