Shugaba Tinubu Ya Taya Janar Babangida murnar Cika Shekaru 83
- Katsina City News
- 17 Aug, 2024
- 321
Shugaban kasa Bola Tinubu ya mika sakon taya murna ga tsohon shugaban mulkin sojin Najeriya, Janar Ibrahim Badamasi Babangida wanda ke cika shekaru 83 a duniya a yau, 17 ga watan Agusta.
A cikin wata sanarwa da ta fito daga Fadar gwamnatin tarayya, shugaba Tinubu ya yaba wa irin gudunmawar da Janar Babangida ya bayar wajen ci gaban Nijeriya, musamman a fannin samar da ababen more rayuwa, inda ya bayyana kammala aikin gadar nan ta Third Mainland Bridge, wadda ita ce gada mafi tsawo a Afirka a lokacin a matsayin aikin da ba za a manta da shi ba.
Shugaban ya kuma amince da irin rawar da Janar Babangida ya taka wajen samar da Najeriya mai tafiya da zamani tare da yaba masa bisa sadaukarwar da yake yi wa kasa.
Shugaba Tinubu ya yi wa tsohon shugaban kasar fatan karin shekaru masu yawa cikin koshin lafiya, inda yake cewa: "Ina taya Janar Babangida murnar shaida wannan lokaci na musamman a rayuwarsa tare da yi masa fatan karin shekaru masu yawa cikin koshin lafiya da farin ciki."
Janar Babangida wanda aka fi sani da IBB ya taba rike mukamin shugaban mulkin sojan Najeriya daga 1985 zuwa 1993.