Yadda ruwan sama yayi sanadiyar rugujewar wasu gidaje a Sabuwar Unguwa cikin garin Katsina.
- Katsina City News
- 17 Aug, 2024
- 285
Daga :-Muhammad Ali Hafizy. Katsina Times.
Akalla an ɗauki kusan kwanaki shidda ana ruwan sama a garin Katsina, wasu kwanakin ana yin ruwan saman ne a cikin dare, amma ruwan yafi yawa a cikin kwanaki uku zuwa biyu da suka gabata.
Wannann dalilin ne ya sanya wasu daɗaddun gidaje waɗanda mafiya yawan su talakawa ne ke rayuwa a cikin su, a cikin Sabuwar Unguwar cikin garin Katsina, iftilain zubewar gidajen ya same su, sakamakon ruwan, masu gidajen sun shaida mana cewa wasu gidajen sun zube a jiya wasu kuma sun zube a yau.
Wasu gidajen sun zube a cikin ƙwaryar cikin gidan kamar dakuna, makewayi da sauransu, yayin da wasu kuma suka zube a wasu ɓangarori na wajen gidan.
Sabuwar Unguwa tana dauke da mutane sosai wadanda suke rayuwa a cikin ta. A gefe guda kuma ana tunanin cewa ba iya Sabuwar Unguwa bace wannann iftila’in ya fada nawa a cikin garin Katsina ba sakamakon ruwan.