Ba Mu Kayyade Farashin Litar Man Fetur Ba, Cewar Ɗangote
- Katsina City News
- 14 Aug, 2024
- 336
Shugabannin da ke kula da matatar man Ɗangote sun ƙaryata rahotannin da ke cewa sun ƙayyade farashin man fetur a kan Naira 600 kan kowace lita.
Sun bayyana hakan a matsayin labarin ƙanzon kurege kuma mara tushe.
Jami’in kula da harkokin kasuwanci da sadarwa na kamfanonin Dangote, Anthony Chiejina ne, ya sanar da hakan a shafinsa X (Twitter) a ranar Laraba.
Ya yi ƙarin haske kan jita-jitar da ake ta yaɗawa na cewar matatar tana tattaunawa da ƙungiyar dillalan man fetur ta ƙasa (IPMAN), kan farashin da za ta fara sayar da fetur.
Kamfanin ya ce bai ƙulla alaƙa da IPMAN ba, ya kuma jaddada cewa duk wani mataki da kamfanin ko matatar ta ɗauka za su sanar a hukumance.
Sanarwar ta cewa “An jawo hankalinmu kan labarin da Jaridar Punch ta wallafa kan cewa kamfanin Dangote ya ƙayyade farashin man fetur kan Naira 600 kan kowace lita, a jiya Talata, 13 ga watan Agustan 2024.”
“Za mu so mu fayyace cewa ba mu da ta wata alaƙar kasuwanci da IPMAN a yanzu,” in ji sanarwar.
Jama’a da dama na dakon lokacin da matatar man fetur ta Dangote za ta fada fitar da kayayyakinta, wanda aka yi hasashen zai sauƙaƙa tsadar da man ke yi a yanzu.
A gefe guda, masana sun ce da zarar matatar ta fara aiki gadan-gadan, hakan zai kawo ƙarshe dogayen layuka da ake samu a gidajen mai.