Shirin 3MTT na Tinubu zai samar wa matasa miliyan uku aikin yi, inji Ministan Yaɗa Labarai

top-news

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya bayyana cewa gwamnatin Tinubu ta shirya tsaf don samar da ayyukan yi miliyan uku ga matasan Nijeriya ta hanyar Shirin 3MTT.

Ministan ya bayyana hakan ne a Abuja ranar Litinin a Taron Matasa ‘Yan Sandan Nijeriya mai taken “Inganta Ƙimar Matasan Nijeriya don Tsaron Ƙasa.”

Ministan, wanda ya samu wakilcin Darakta Janar na hukumar gidan rediyon Muryar Nijeriya (VoN), Malam Jibrin Baba Ndace, ya ce shirin na 3MTT, wanda Ma’aikatar Sadarwa ke jagoranta, wani shiri ne na ilimi da ƙwarewar da za su inganta iyawa da ƙimar matasa a harkar tsaron ƙasa.

Ya ce: “Shirin 3MTT tabbaci ne na burin Shugaba Tinubu na samar da cigaban matasa a cikin dabarun cigaban ƙasa baki ɗaya. Domin samar da kyakkyawan tsari don cimma wannan, gwamnatin tana kuma ba da fifiko ga tattalin arzikin matasan Nijeriya, wajen gina ƙasa mai tsaro da wadata.” 

Idris ya ce kafa Asusun Ba Da Lamuni na Ilimi na Nijeriya (NELFUND), wanda a halin yanzu yake bayar da lamuni da tallafin kuɗi ga ɗaliban Nijeriya, yana ɗaya daga cikin manyan tsare-tsare a ƙarƙashin Shirin Sabunta Fata na Shugaba Tinubu, da nufin yin tasiri sosai kan neman ilimi na matasa.

A yayin da yake magana kan tsadar sufuri a ƙasar nan, ministan ya ce Shugaban Ƙasa ya ɓullo da shirin CNG don amfani da isasshiyar iskar gas da ƙasar ke da ita wajen rage farashin sufuri da kusan kashi 70.

Ministan ya kuma jaddada buƙatar da ke akwai ta matasa su yi koyi da kyawawan ɗabi’un da suka dace domin su taka rawar su a harkar tsaron ƙasa.

Sai dai ministan ya gargaɗi matasa kan illolin da yaɗa labaran ƙarya ke da shi ga tsaron ƙasa, yana mai cewa wannan muguwar ɗabi’a amfani da ‘yancin faɗin albarkacin baki, wanda gwamnati mai ci yanzu ta amince da shi, ta hanyar da ba ta dace ba ne.

Ya ce: “Inda aka ba da yawa, ana sa ran da yawa. Dole ne mu yarda cewa yaɗa labaran ƙarya ya haɗu da babbar barazana ga tsaron ƙasa, wadda ta haɗa da tada hankali, rashin zaman lafiya, laifuffuka na ƙasa da ƙasa, ta'addanci, fashi da makami, tsattsauran ra'ayi, da munanan ayyukan da ake yaɗawa ta hanyar intanet."

NNPC Advert