Gwamnatin Jihar Katsina Ta Dage Dokar Hana Fita Bayan An Samu Zaman Lafiya
- Katsina City News
- 13 Aug, 2024
- 252
Katsina, Najeriya - 13 Ga Agusta, 2024
Mukaddashin Gwamnan Jihar Katsina, Malam Faruk Lawal, ya sanar da dage dokar hana fita da aka kafa a fadin jihar. Wannan mataki ya biyo bayan rahotanni ne da suka nuna dawowar zaman lafiya da kwanciyar hankali a duk fadin jihar.
Sakataren Gwamnatin Jihar, Abdullahi Garba Faskari, ya bayyana wannan ci gaban, yana mai cewa dage dokar hana fitan na da nufin bai wa 'yan ƙasa damar ci gaba da gudanar da ayyukansu na yau da kullum ba tare da cikas ba.
Duk da cewa an samu ingantaccen yanayin tsaro, hukumomi sun yi kira ga mazauna jihar da su kasance cikin shirin ko-ta-kwana tare da kai rahoton duk wani motsi da ba a saba gani ba ga hukumomin tsaro da suka dace.
A cikin jawabinsa, Mukaddashin Gwamna Lawal ya sake jaddada kudirin gwamnatin jihar karkashin jagorancin Gwamna Dikko Radda na magance kalubalen tsaro da ake fuskanta. Ya nuna godiyarsa ga hukumomin tsaro da al'ummar jihar Katsina bisa hadin kai da goyon bayan da suka bayar.
Gwamna Lawal ya kuma yi kira da a ci gaba da yin addu'o'i da haɗin kai, yana mai jaddada cewa zaman lafiya mai dorewa ne zai bai wa jihar damar samun ci gaba mai ma'ana.