"Mu Hada Kai Domin Tunkarar Zabe Mai Zuwa" Inji Tsohon Danmajalisar tarayya a PDP, Aminu Chindo

top-news



Zaharaddeen Ishaq Abubakar, Katsina Times

Tsohon dan majalisar wakilan Najeriya, Alhaji Aminu Ahmed Chindo (Sadaukin Katsina), ya yi kira ga zababbun shugabannin jam'iyyar PDP na ƙaramar hukumar Katsina da su hada kai domin tunkarar zaben kananan hukumomi da za a gudanar a shekarar mai zuwa.

Chindo ya yi wannan kiran ne a ranar Asabar, lokacin da tawagar zababbun 'ya'yan jam'iyyar PDP na ƙaramar hukumar Katsina suka kai masa ziyara bayan kammala zaɓen shugabanni.

Tsohon dan majalisar ya yi kira ga jagororin jam'iyyar a matakin ƙaramar hukuma da su kasance masu haƙuri, riƙe sirri, da kuma haɗin kai domin cimma nasara a zabukan da ke tafe.

Ya ce, "Tabbas, kowa ya san halin da ƙasar nan ke ciki, a irin wannan yanayin al'umma mu suke so. Babu shakka muna da kwarin gwiwa kan samun nasara a zaben kananan hukumomi da za a gudanar. Mun samu labarin cewa har suna tunanin sauya wasu 'yan takara saboda sun gano cewa ba su da ingantattun 'yan takara."

Ya yaba wa Honorable Yasir Abubakar, wanda yake takarar shugabancin ƙaramar hukumar Katsina, bisa ƙwarewarsa da riƙon amana, tare da iya jagoranci.

Tun da farko, sabon zaɓaɓɓen shugaban jam'iyyar PDP na ƙaramar hukumar Katsina, Alhaji Ibrahim Galadima, ya bayyana yadda zaɓen ya gudana bisa tsari, tare da samun shaidu daga ɓangarorin tsaro a jihar Katsina, wanda ya kai shi ga zama shugaban jam'iyyar tare da sauran mataimakansa bakwai da National Delegate.

NNPC Advert