Gwamnati Ta Saki Matasan da Aka Kama a Zanga-zanga — Comrade Bilal Lawal Kurfi
- Katsina City News
- 10 Aug, 2024
- 441
Comrade Bilal Lawal Kurfi ya yi kira ga gwamnatin da ta saki matasan da aka kama yayin zanga-zanga. Ya bayyana haka ne a wajen bikin rantsar da kwamitin gudanar da zaɓen ƙungiyar ɗalibai ta ƙasa (NANS) reshen Arewa maso Yamma (Zone A), wanda aka gudanar a ranar Asabar, 10 ga Agusta, 2024, a babban ɗakin taro na makarantar Muhammadu Buhari Metrological Institution, Katsina.
Babban bako a wajen taron, Shugaban Hukumar Bayar da Tallafin Karatu ta Jihar Katsina, Dr. Aminu Salisu Tsauri, ya yabawa ƙungiyar bisa ƙoƙarinta na kare haƙƙin ɗalibai, yana mai jaddada muhimmancin aikin kwamitin da aka rantsar. Ya kuma shawarci sabbin shugabannin da su yi amfani da damar wajen sauke nauyin da aka ɗora musu.
A nasa jawabin, Mataimakin Gwamna akan Harkokin Dalibai, Hon. Muhammad Nagaske, ya nuna farin cikinsa game da yadda aka gudanar da taron, yana mai fatan ganin ci gaban ƙungiyar a nan gaba.
Shugaban ƙungiyar na Arewa maso Yamma ya yi kira ga gwamnati da ta sake duba batun matasan da aka kama yayin zanga-zanga, yana mai neman su a sake su. Ya kuma godewa Allah bisa nasarar da ya samu na sauke nauyin da aka ɗora masa na tsawon lokaci, tare da yi wa sabbin shugabanni fatan alheri a gudanar da sahihin zaɓe.
Bayan kammala taron, an karrama mutane da dama waɗanda suka bayar da gudummawa ga ci gaban dalibai, ciki har da Dr. Aminu Salisu Tsauri, Hon. Muhammad Nagaske, da kuma Guga Global Foundation.