Matasan Najeriya Sun Kudurta Shirye-Shirye Don Samun Sauyin Shugabanci a Zaben 2027
- Katsina City News
- 10 Aug, 2024
- 533
Nura Yau Marabar Musawa ya bayyana cewa matasan Najeriya sun fara shirin tsaf domin tabbatar da samun sauyin shugabanci mai inganci a kakar zaben 2027. Ya ce matasa na taka muhimmiyar rawa wajen gina al'umma, amma duk da haka, sun fuskanci kalubale masu yawa a halin yanzu, ciki har da rashin tsaro, tsadar rayuwa, da kuma rashin aikin yi.
A cewar Nura, Najeriya tana da arziki mai tarin yawa kuma tana da dimbin matasa. Duk da haka, baiwa matasa damar shiga harkokin tafiyar da mulki ya yi matukar raguwa, musamman bayan shugabancin marigayi Umaru Musa Yar'Adua da Goodluck Jonathan, wadanda suka yi fice a lokacin da suke matasa.
Nura ya bayyana yadda rashin tsaro a yankin arewacin ƙasa, da kuma tsadar rayuwa, suka sanya matasa cikin kunci. Duk da cewa matasa da yawa suna da ilimi mai zurfi, gwamnati ta kasa samar musu da aikin yi, lamarin da ya kara tsananta matsalolin tattalin arziki.
Yanzu haka, wasu daga cikin matasan Najeriya sun shirya zanga-zanga daga ranar 1 ga watan Agusta zuwa 10 ga watan Agusta, 2024, domin neman gwamnatin ta biya musu bukatunsu. Sun bayyana cewa suna da kyakkyawar aniyar samar da sauyi mai inganci domin gina ƙasa mai kyakkyawar makoma.
Nura ya yi kira ga matasan Najeriya da su hada kai, su juriya, tare da yin addu’a don ganin tafiyar tasu ta cimma nasara. Ya roki Allah da ya kawo sauyi mai kyau ga Najeriya tare da kare ta daga dukkan wata barna.