Gwamnatin Jihar Katsina Ta Sassauta Dokar Hana Fita a Fadin Jihar
- Katsina City News
- 10 Aug, 2024
- 540
Gwamnatin Jihar Katsina ta sanar da sassauta dokar hana fita da aka kakaba a duk fadin jihar.
Dokar hana fitan da ta fara aiki daga karfe 7:00 na yamma zuwa 7:00 na safe, yanzu an sassauta ta zuwa daga karfe 10:00 na dare zuwa 5:00 na safe a fadin jihar.
Sakataren Gwamnatin Jihar, Abdullahi Garba Faskari, ya bayyana cewa mukaddashin gwamnan jihar, Malam Faruk Lawal, HCIB, ya gamsu da rahotannin ingantuwar tsaro a duk fadin jihar, wanda ya sa ya umarci a sake duba dokar hana fita tare da aiwatarwa nan take.
Malam Faruk Lawal ya yaba wa jami’an tsaro bisa kyakkyawan kokarinsu da kuma hadin kan al’umma yayin da gwamnati ke kokarin shawo kan lamarin tsaro.
Ya kuma yi kira ga al’umma da su ci gaba da bin doka tare da gudanar da harkokinsu na yau da kullum cikin lumana.