Gwamnan Ebonyi: Daga Mai Gini Zuwa Shugaban Jihar
- Katsina City News
- 10 Aug, 2024
- 426
Zaharaddeen Ishaq Abubakar, Katsina Times
A shekara ta 2010, Gwamnan Jihar Ebonyi ya dauki hoton nan tare da matarsa da dansa. A wancan lokacin, shi mai gini ne a garinsu na Izzi. Amma a shekarar 2011, wani mutum ya taimake shi, ya dauki nauyin takarar sa, ha yaci zabe a matsayin dan majalisar dokoki ta Jihar Ebonyi, inda daga bisani ya zama Kakakin Majalisar.
A cikin wannan nasara, tsohon Gwamna ya zabe shi a matsayin dan takarar gwamna karkashin jam’iyyar APC, kuma yau shi ne Gwamnan Jihar Ebonyi. An samu labarin cewa ya rubuta jarabawar takardar shaidar kammala makarantar sakandare (SSCE) lokacin da yake cikin majalisar dokokin jihar.
Ba wanda zai iya cewa wa matarsa a lokacin da suka yi aure cewa mijin da take tare da shi mai gini ne zai zama gwamna a cikin 'yan shekaru kadan.
Duk da cewa iyayenta sun kai ta makaranta kuma ta fito daga gidan da ke da arziki, sai ta auri talaka mai gini don samun abinci.
Wannan labari yana kara mana karfin gwiwa, domin gobe ta fi kowa girma. Kada ka kalli kanka bisa yanayin da kake ciki a yanzu, domin shekara daya na iya sauya maka labari. Ka ci gaba da yin kokari!