Ana Zargin Wasu Sojoji da Raba Tutar Kasar Rasha ga Masu Zanga-Zanga a Katsina
- Katsina City News
- 08 Aug, 2024
- 369
Daga Wakilanmu @ Katsina Times
Majiyoyi daban-daban a hedkwatar ‘yan sanda ta jihar Katsina sun tabbatar wa jaridar Katsina Times cewa, ‘yan sanda sun kama wasu sojoji biyu da ake zargi da raba tutar kasar Rasha ga masu zanga-zangar tsadar rayuwa don su daga ta yayin zanga-zangar.
Majiyarmu ta bayyana cewa an kama wadanda ake zargin a yankin karamar hukumar Funtua ta jihar Katsina. A cewar majiyar, ana zargin sojojin suna cikin aiki amma sun dauki hutun aiki daga barikinsu.
Majiyarmu ta tabbatar da cewa binciken farko da aka yi a ofishin ‘yan sanda na Funtua ya tabbatar da cewa akwai alamun gaskiya kan zargin, kuma sojojin har yanzu suna cikin aiki duk da suna kan hutun gida.
Binciken ya ci gaba da kasancewa karkashin hedkwatar ‘yan sanda ta jihar Katsina, inda ake ci gaba da gudanar da bincike kan lamarin.
Mun yi ƙoƙarin jin ta bakin mai magana da yawun ‘yan sanda, amma ba mu samu nasara ba.