Abin da ya kamata mutane su sani game da kudin da ake cewa gwamnatin tarayya ta ba gwamnonin jihohi
- Katsina City News
- 06 Aug, 2024
- 495
Yana da kyau mutane su yi bincike su gano hakikanin abin da ya faru kan wani lamari kafin su fara magana a kansa domin gudun da na sani daga baya. Hakika akwai wasu kudade da jihohi ke sa ran za su samu (ba su ma kai ga zuwa asusunsu ba). Wadannan kudi, kudi ne na shirin da ake kira Nigeria Community Action for Resilience and Economic Stimulus Program (NG-CARES) daga Babban Bankin Duniya (World Bank) da idan suka isa kowace jiha, jagororin jihar za su lakaba musu irin sunan da suke so. A jihar Katsina, wannan shirin ana kiran sa da KT-CARES da zai farfado da bangarori daban-daban da ke bukatar daukin gaggawa.
Wadannan kudade da ake ta yamadidi a kansu dai daga bankin duniya suke wato 'World Bank' da kowace jiha za ta yi ayyukan raya kasa wanda daga bisani su Bankin Duniya zasu turo mutanen su domin su duba aikin. Idan aikin ya gamsar dasu kuma ya cika ka’idoji zasu biya Jihar kudin aikin sannan zasu basu kyautar kudade domin sunyi abun da ya dace abun da ake kira a turance “Project for Result”. Wannan akasin labarin dake yawo a kafafen sadarwa Zamani akan cewa shugaba Tinubu yana jihohi kudade.
A zantawar da nayi da Kwamishinan Kasafin Kudi da tsare-tsare na Jihar Katsina, Hon. Bello Hussaini Kagara, ya shaida mani cewa a jihar Katsina, an samu jimillar kudi N15,455,420,486,35 a karkashin wannan shiri. Ga kuma yadda gwamnatin Malam Umar Dikko Radda PhD ta tsara yadda za ta kashe wa al'ummar jihar Katsina su Wanda ta tura ma Majalisar Dokoki Jihar Katsina domin amincewa kafin aiwatar da aiki:
1- An ware Naira bilyan 10 don aiwatar da manyan ayyuka a cikin wadannan kudi, domin al'ummar jihar Katsina su amfani wannan tallafi na bankin duniya.
2- Sannan, an ware N1,500,000,000 don biyan wani bangare na basukan da jihar Katsina ke bi. A lokacin da wannan gwamnatin ta karbi ragamar tafiyar da jihar Katsina, ta zuba jimillar wadannan kudi domin kada shirin ya tsaya.
3- Bugu da kari, akwai N1,250,000,000 don aiwatar da aiki shirin raya karkara na CSDA da ya hada da gyaran asibitocin yankunan karkara, gina azuzuwa, gina hanyoyi da kwalbatoci da ma sauran ayyukan raya karkara.
4- Haka kuma, akwai N1,900,000,000 don aiwatar da shirin Fadama da ya hada da rarraba takin zamani, maganin feshin kwari, kungiyoyin masana’antu da raba awaki don kiwo ga mata musamman na yankunan karkara.
5- Kuma, an ware N400,000,000 Wanda za’a zuba ta a hukumar kula da kanana da matsakaitan masana'antu ta jihar Katsina (KASEDA) domin bunkasa kananan masana’antu.
6- Sannan an ware N405,000,000 ta aikin Kwamitin gudanarwa na shirin da zai sa ido kan yadda da shirin zai gudana. Wannan sun hada da gina sakatariyar da shirin zai yi amfani da ita don gudanar da aikinsa da kudaden gudanarwa da sayo motocin zirga-zirga da zasu zagaya dukkanin Kananan Hukumomi da sauran kayan aikin da za a rika gudanar da shirin.
Kuma duk wannan lissafin, ba za a iya kashe sisin-kwabo a cikin kudin ba, har sai Majalisar Dokoki ta amince da hakan. Wannan ne ya sa Mai Girma Gwamna Malam Dikko Umaru Radda ya aike da neman Majalisar Dokoki ta amince ta hanyar tura mata kasafin kudin cike gibi wato "Supplementary Budget". A halin da ake ciki, majalisar dokoki ta amince, har ta maido wa Gwamna, ya ma sanya hannu a kai, da hakan zai ba gwamnatin jihar damar kashe wadannan kudade domin amfanimsu ya isa ga talakawan jihar Katsina.
Ina mai tabbatar muku, maganar nan da nake yi da ku, yanzu haka wadannan kudi, ba su ma kai ga shiga asusun gwamnatin jihar Katsina ba. Tabbacin shi ne, jihar Katsina ta kammala cika dukkanin wasu ka'idoji na samun wadannan kudade kuma tana fatar za su shigo domin hidimta wa al'ummar jihar Katsina.
Isah Miqdad,
6 ga watan Agusta, 2024.