BINCIKEN MUSAMMAN: GWAMNATIN KATSINA TA YI ƘOƘARI DON HANA ZANGA-ZANGA TA RIKIƊE ZUWA RIKICI
- Katsina City News
- 03 Aug, 2024
- 513
ABIN TAKAICI GA ZABABBUN MU
Daga Jaridun Katsina Times da Taskar Labarai
Wani bincike da jaridun Katsina Times suka gudanar ya tabbatar da ƙoƙarin da gwamnatin Katsina ta yi na ganin duk wata zanga-zangar da za a yi a jihar Katsina ta gudana cikin lumana da kwanciyar hankali.
Binciken ya tabbatar da cewa babban ƙuduri da manufar da gwamnatin ta ɗauka shi ne ganin ba a fasa shaguna ko lalata dukiyar gwamnati ba, ko da kuwa za a yi wannan zanga-zangar.
Alhaji Farouƙ Lawal Jobe, mataimakin gwamna kuma mukaddashin gwamna a yanzu, da shugaban ma'aikata a gidan gwamnatin Katsina, Alhaji Jabiru Tsauri, da sakataren gwamnatin Katsina, Barrista Faskari, sun yi aiki tukuru ba dare ba rana.
Hatta gwamnan Katsina zababbe, Malam Dikko Umar Raɗɗa, yana sa ido awa 24 kan abin da ke faruwa a Katsina. Majiyarmu ta tabbatar mana duk wani mataki da za a ɗauka sai an sanar da shi, don haka yana sane da me ake ciki ɗari bisa ɗari.
Mun tabbatar akwai wasu wuraren da Gwamnan na Katsina, Malam Dikko Umar Radda, PhD, ya saka baki da kansa domin a tabbatar da jihar ta zauna lafiya.
Gwamnatin ta yi tarurruka daban-daban da ƙungiyoyi da ɗaiɗaikun mutane domin ganin cewa lallai an roƙi matasa in za a fito, to a fito cikin lumana.
Shugaban ma'aikata na gidan gwamnatin Katsina, Alhaji Jabiru Tsauri, har lungu da saƙo-saƙo na birni ya riƙa bi don ganin an roƙi matasa su tabbatar ba a yi ƙone-ƙone da satar kayan mutane ba. Wannan zirga-zirga da aka tarar matasa har gida ya taimaka sosai.
Ofishin Mukaddashin Gwamna, Alhaji Farouƙ Jobe, ya tabbatar an ɗauki matakin dakile yaɗa hotunan ƙarya da bidiyo tsofaffi, ko na wasu garuruwa, a danganta su da jihar Katsina.
Yaɗa labari da hotunan ƙanzon-kurege na cikin abin da ke faɗaɗa rikicin zuwa inda bai kai ba.
A ranar da za a yi zangar, gwamnatin Katsina ta halarci taron addu'a na shekara-shekara da ake yi mai suna Yaumul Shukkur, duk manyan malaman Katsina ko wakilansu suna wajen.
Da yammacin ranar, Gwamnan Katsina ya gana da 'yan ƙungiyoyin farar hula, kuma a ranar ya gana da manema labarai, inda Gwamnan Katsina na riko ya ce, 'yan jarida ku shaida ne a Katsina ba a fasa shagon kowa ba, ba a ƙona wajen gwamnati ba. Farar hula sun yi jerin gwanonsu cikin lumana, sun kuma ba mu takarda. Za mu kuma miƙa ta ga gwamnatin tarayya.
Ya ce, 'yan kalilan da suka so tada hatsaniya ba su a cikin matasa na gari da suka shirya zanga-zangar lumana don bayyana halin da ake ciki na ƙuncin rayuwa.
ABIN TAKAICI
Wani abin takaici da binciken mu ya tabbatar shi ne, sam duk zababbun da muke da su ba wanda muka gani a mabazarsa yana irin ƙoƙarin da gwamnatin jiha ta yi tun daga sanatoci har zuwa kansilolin Katsina.
Gwamnatin jiha aka bari ita kaɗai ke ɗaukar bugun.
A iya binciken mu, ba wani sanata ko ɗan majalisar tarayya da muka gani a jihar yana ganawa da mutanen mazabarsa yana roƙon alfarma na kauce wa zanga-zangar da za ta kawo fitina, ba mu gani ba ko ɗaya.
Hatta zababbun 'yan majalisun jiha ba mu ga ko ɗaya a ƙaramar hukumarsa ba yana neman alfarma da roƙon in har za a yi kar a bari ya koma rikici.
Mafi yawansu mafaka suka nema suka boye.
GWARAZAN NASARA
Tarihi ba zai taba mantawa da ƙoƙarin da waɗannan mutane suka yi ba na ganin cewa jihar Katsina ba ta faɗa ƙone-ƙone da sace-sace ba a zanga-zangar lumana ta ƙasa da aka shirya a jahar Katsina.
1. Malam Dikko Umar Raɗɗa, PhD, ya riƙa waya da bin me ke faruwa da yi wa wasu magana waɗanda ba su cikin gwamnati su yi wani abu da zai hana barkewar rikici.
2. Alhaji Farouƙ Lawal Jobe, shi ne mukaddashin gwamna a lokacin, ya sanya ido da aiki ba dare ba rana ganin lamarin bai rincabe ba.
3. Alhaji Jabiru Tsauri, shugaban ma'aikata na gidan gwamnatin Katsina, ya sanya an riƙa bin matasa unguwa-unguwa ana roƙonsu kar su yi ƙone-ƙone ko sace-sace.
4. Barrista Abdullahi Faskari, sakataren gwamnatin jihar Katsina.
5. Akwai malamai na Allah da suka riƙa ba da shawara ta Allah.
6. Akwai ƙungiyoyin farar hula na gaskiya da suka tsara zanga-zangar lumana mai ma'ana, kuma cikin tsari da kamala. Suka kuma ba gwamnatin jiha takarda zuwa ga shugaban ƙasa.
TAMBAYA:
Me ya hana zababbunmu zuwa ga jama'ar da suka zabe su? Tun daga Kansila har zuwa Sanata?