GWAMNAN ZAMFARA DAUDA LAWAL YA ƘADDAMAR DA FARA RABON TALLAFI
- Katsina City News
- 06 Sep, 2023
- 842
-YA CE, BA RABON SIYASA BA NE, KOWA ZAI AMFANA
Gwamna Dauda Lawal, a yau Talata ya ƙaddamar da rabon kayan abinci a matsayin tallafi ga al’ummar Jihar Zamfara.
Yayin ƙaddamar da wannan bayar da tallafi, Gwamna Lawal ya yi kira ga kwamitin da ke da alhakin rabon tallafin da su yi aiki tsakaninsu da Allah.
Mai magana da yawun gwamnan na Zamfara, Sulaiman Bala Idris, a wata sanarwar manema labarai da ya fitar a Gusau, ya ce wannan tallafi na daga cikin matakan farko don ragewa mutane raɗaɗin janye tallafin man fetur da gwamnatin tarayya ta yi.
Ya ƙara da cewa, gwamnatin tarayya ta bayyana za ta ba jihohi bashin Naira Biliyan 5.
Takardar ta ci gaba da cewa: “A jawabinsa yayin ƙaddamar da tallafin, Gwamna Lawal ya ja hankalin membobin wannan kwamiti da su sa tsoron Allah gaba da komi.
“Cikin jawabin, gwamnan ya ce gwamnatin Zamfara za ta ɗauki mataki a kan duk wani wanda aka kama da laifin karkatar da wannan tallafi.
“A cikin Naira biliyan 5 da gwamnatin tarayya ta ce za ta ba jihohi bashi, Jihar Zamfara ta samu Naira biliyan biyu, da buhun shinkafa dubu 11, 877 da kuma buhun shinkafa 2, 834, wanda za ta raba su ga ƙananan hukumomi shida.
“Sashe na biyu na wannan tallafi za a gabatar da shi ga ƙananan hukumomi takwas wanda za a fara da zaran gwamnatin ta amshi wannan tallafi daga gwamnatin tarayya.
“Mataimakin Gwamna, Mallam Mani Mallam Mummuni shi ne zai jagoranci kwamitin da zai yi wannan rabon tallafi ga al'umma.
“Kowacce ƙaramar hukuma za ta samu buhun shinkafa 2, 000. Buhunan Taki da amfanin gona.
“Haka kuma gwamnatin za ta fara bayar da tallafin karatu ga ɗalibai ‘yan asalin jihar Zamfara.”