DSS sun kama Kabir Shehu Yandaki bayan jagorantar zangar zangar yunwa a Katsina.
- Katsina City News
- 02 Aug, 2024
- 676
Daga Comr Nura Siniya
Jami'an tsaro na farin kaya DSS sun kama matashin dan gwagwarmaya sakataren gamayyar kungiyoyin fararen hula na jihar Katsina Comrade Kabir Shehu Yandaki bayan jagorantar zanga zangar tsadar rayuwa a jihar Katsina.
Matashin Comrade Kabir Shehu Yandaki, yana daga cikin matansan da suka jagoranci zanga zangar yunwa da aka fara gudanarwa a Najeriya
Wannan kamu da DSS suka yi mashi yana zuwa ne bayan sa'o'i 24 da jagorantar zanga zangar tsadar rayuwa a jihar Katsina.