Gwamna Dauda Na Zamfara ya bukaci hadin kan Malamai don ciyar da jihar gaba

top-news

Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal ya buƙaci Majalisar Malamai ta Jihar Zamfara da su haɗa kai da gwamnatinsa domin cetowa tare da sake gina jihar.

Gwamnan ya yi wannan kiran ne a yayin ƙaddamar da Majalisar Tuntuɓar Malamai ta Jihar Zamfara, wanda ya gudana a ranar Talata a ɗakin taro da ke gidan gwamnati a Gusau.

A wata sanarwa da Mai Magana Da Yawun Gwamnan, Sulaiman Bala Idris, ya fitar a Gusau yau, ta jaddada muhimmiyar rawar da majalisar ke takawa wajen bayar da shawarwari kan yadda gwamnati za ta yi daidai da tsarin addini.

Ya ƙara da cewa, a cikin shekaru 21 da suka gabata Majalisar Malamai ta bayar da gudunmawa mai ƙarfi ga jiha da al’ummar Zamfara, inda ta nuna irin tasirin da ta ke da shi a matakin gwamnati.

Da yake gabatar da jawabi, Gwamna Lawal ya tabbatar wa Majalisar cewa ƙofofinsa a buɗe suke a kodayaushe domin karɓar shawarwari masu muhimmanci kan al’amuran da suka shafi manufofin jiha da kuma jin daɗin al'umma.

“Yayin da muka taru a nan a yau, ina cike da godiya mai yawa ga Allah Maɗaukakin Sarki da ya ba mu damar ƙaddamar da sabuwar Majalisar Malamai da aka sake kafawa.

“Wannan Majalisar da aka fi sani da Majalisar Shawarar Malamai, an kafa ta ne a shekarar 2003 a matsayin wata cibiya mai muhimmanci a yunƙurin gwamnati na ƙarfafa aiwatar da Shari’a a Jihar Zamfara. Majalisar ta ƙunshi fitattun malaman addinin Musulunci, kuma tana jagorantar al'ummarmu ta fuskar ɗabi'a, tarbiyya da tattalin arziki.

“Dokar kafa majalisar wacce ita ce doka mai lamba 6 ta shekarar 2003, ta fayyace komai dalla-dalla, da dai sauransu, kan ayyukan majalisar.

“Wasu daga cikin ayyukan su shi ne tantancewa, ba da shawarar cancanta da kuma dacewa da mutumin da za a naɗa a matsayin Alƙalin Kotun Shari’a.

“Bayar da amsa ga tambayoyi (fatawa) ko mas’aloli a cikin fikihun Musulunci.

“Karɓar sakamakon binciken da ya shafi sabbin abubuwan da ke fitowa daga ci gaban fasaha da sauran batutuwan zamani.

“Nasiha ga Gwamna kan daidaito ko akasin haka da ƙa’idojin Shari’a dangane da duk wani ƙudiri na doka.

Bugu da ƙari, gwamnan ya buƙaci malaman addini da su ci gaba da sauke nauyin da ya rataya a wuyansu cikin himma, jajircewa, da kuma sanin ya-kamata bayan an sake gyara tare da ƙaddamar da majalisar.

“Dukkanku manyan malaman addinin Musulunci ne da al’umma ke neman shiriya ta ɗabi’a daga wurin ku. Bai kamata ku huta ba wajen sauke nauyin da aka ɗora muku na majalisar malamai da kuma ginshiƙan al'umma."

NNPC Advert