Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal ya amince da aikin hanyar Magami zuwa Ɗansadau mai tsawon kilomita 108.
- Katsina City News
- 30 Jul, 2024
- 445
Gwamnan ya amince da aikin hanyar ne yayin da ya jagoranci taron Majalisar Zartarwa ta Jihar Zamfara a ranar Litinin da ta gabata a gidan gwamnati da ke Gusau.
A cikin wata sanarwa da Mai Magana da Yawun Gwamnan, Sulaiman Bala Idris, ya fitar ta bayyana cewa, an ɗauki aikin hanyar Magami zuwa Ɗansadau ne a matakin gaggawa domin magance matsalar tsaro da kuma bai wa al’ummar yankin fifiko don jin daɗin rayuwar su.
Sanarwar ta ƙara da cewa, a tarona majalisar zaryarwar, an tattauna muhimman batutuwa da suka haɗa da yadda ake gudanar da kasafin kuɗi.
“Gwamna Dauda Lawal ne ya jagoranci zaman Majalisar Zartarwa ta Jihar Zamfara, wanda ya gudana jiya.
“A taron, gwamnan ya amince da sake gina hanyar Magami zuwa Ɗansadau.
“Aikin titin mai tsawon kilomita 108, kamar yadda aka bayyana a cikin kasafin kuɗin shekarar 2024, ma’aikatar ayyuka da samar da ababen more rayuwa ta samu amincewar gwamnan na fara aikin, tare da bin tsarin da ya dace na bayar da kwangila, da ba da izini da kuma takardar shaidar aiki ba tare da wata matsala ba daga Hukumar Sayen Kayayyakin Gwamnatin (BPP).
“Gwamnan ya amince da bayar da kwangilar ga kamfanin 'Dantata and Sawoe Construction Co. Ltd', a matsayin kwangilar da za a yi ta cikin watanni 18 a kan kuɗi Naira 81,189,223,505.73.”
Manyan abubuwan da aikin ya ƙunsa sun haɗa da; tsaftace dukkan wuraren da aikin zai shafa, cire kayan da ba su dace ba da maye gurbinsu, tare da ingantattun kayan da aka yarda da su, da samar da magudanan ruwa ingantattu, da sanya gadoji a wuraren da suka dace.