Tsohuwar Kwamishinan Ilimi ta jihar Katsina ta Cire Kayan Tsohon Ofishin ta

top-news

Katsina Times

Jaridar Katsina Times ta tabbatar da cewa tsohuwar kwamishinar ma’aikatar ilimi ta jihar Katsina, Hajiya Hadiza Abubakar, ta cire wasu kayan ofishin da ta bari a ma’aikatar ilimi bayan an canza ta zuwa ma’aikatar mata.

Katsina Times ta gano cewa an cire kyanren da ta sanya wanda yake mai tsadar gaske da ke amfani da fasahar dan yatsa kafin a buɗe shi. Haka kuma, tsohuwar kwamishinar ta sanya bidiyon CCTV a ma’aikatar ilimi, wanda ana zargin ta cire shi bayan ta tashi daga ofishin.

Wani na kusa da tsohuwar kwamishinar da aka canza wurin aikinta ya bayyana cewa duk abin da ta cire daga ofishin kayan ta ne da ta siya da kudin kanta, ba kudin gwamnati ba.

Wani jami’i a ma’aikatar ilimi, wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya ce a ka’ida ba a amfani da kudin kashin kai wajen gyaran ofis sai dai idan an nemi a sake biyanka.

Ma’aikatan ma’aikatar ilimi sun nuna farin ciki da jin dadi da canza wurin aikin tsohuwar kwamishinar, suna tuna yadda farkon zuwanta ta hana yin sallah a wani wajen da aka shafe sama da shekaru ashirin ana sallah ba tare da bayyana dalili ba.

Ma’aikatan sun kuma rika koke da shigar ta na kayan da ke saba ma al’ada da kuma horon malaman makarantun jihar Katsina.

Labarin ta ya watsu a Katsina, musamman a wani bidiyon ziyarar ta zuwa fadar mai martaba Sarkin Katsina, Alhaji Abdulmumini Kabir Usman CFR, wanda har sarkin Katsina yayi mata nasiha.

Mun yi kokarin jin ta bakin kakakin ma’aikatar ilimi ta jihar Katsina amma bamu samu ba. Mun kuma yi kokarin jin ta bakin kwamishinar mata na yanzu, amma wayarta bata shiga kuma sakon da muka aika mata ba a amsa ba.

Katsina Times

[www.katsinatimes.com](http://www.katsinatimes.com)
Jaridar Taskar Labarai
[www.taskarlabarai.com](http://www.taskarlabarai.com)
All Social Media Platforms

NNPC Advert