Masu shirin zanga-zanga a Nigeria na fuskantar barazana daga Gwamnati - Amnesty
- Katsina City News
- 30 Jul, 2024
- 416
Ƙungiyar kare haƙƙin ɗan'adam ta Amnesty International ta yi gargaɗin cewa yin barazana ga masu shirin gudanar da zanga-zanga ba tsari ba ne na dimokuraɗiyya.
Yekuwar zanga-zangar da aka shirya gudanarwa daga daga ranar 1 ga watan Agusta mai kamawa, ta samu karbuwa a shafukan sada zumunta da kuma wasu ‘yan kasar.
Majiya Jakadiya ta BBC, ta bayyana cewa, Hukumomin Najeriya sun yi gargaɗi kan gudanar da zanga-zangar da za ta jefa ƙasar cikin tashin hankali tare da yin kwatanci da halin da ƙasashe kamar Kenya da Sudan da Libya ke ciki sakamakon yin bore.
Sai dai duk da cewa gwamnatin Najeriya ta ce ƴan ƙasar na da ƴancin yin zanga-zanga ta lumana, amma shugaban kungiyar CISLAC kuma babban jami'i a kungiyar Amnesty International a Najeriya, Auwal Musa Rafsanjani, ya ce "Dimukuradiyya ta ba ƴan ƙasa ƴancin fitowa su nuna damuwarsu.
"Zanga-zanga tana ɗaya daga cikin tsarin mulkin ɗimokuraɗiyya da muke bi domin ko shi shugaban ƙasa na yanzu ta taɓa yin bara'a ga tsarin tafiyar da gwamnati."
Yi wa masu zanga-zangar barazana, zai gurgunta nasarorin Shugaba Bola Tinubu da ya samu a baya," in ji Rafsanjani.
Ya ƙara da cewa idan har gwamnati ba ta son a yi zanga-zanga, ya kamata ta gaggauta yin gyara.
"Ya dace a ce Gwamnati ta ƙara jaddada wa ƴan Najeriya cewa da gaske take yi wajen kawo gyara ga matsalolin da suka addabi ƴan Najeriya musamman tsadar rayuwa - wane tsari aka kawo da aka cire kuɗin tallafin mai," in ji shi.