Kungiyar Bayar Da Agajin Gaggawa Mai Suna "Association Of First Aid Group Of Nigeria" Yankin Jihar Katsina, Sun Gudanar Da Taron Cika Shekara Biyu Da Kafuwar Kungiyar.

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes28042025_092425_FB_IMG_1745832193218.jpg


Daga:- Muhammad Ali Hafizy, @Katsina Times.

Hadaddiyar kungiyar bayar da agajin gaggawa mai suna "Association Of First Aid Group Of Nigeria" yankin jihar Katsina, sun gudanar da taron cika shekaru biyu da kafuwar kungiyar a ranar Lahadi 27 ga watan Afrilu na shekarar 2025, a shelkwatar addini dake bisa titin Kofar Sauri cikin jihar Katsina.

Taron wanda aka shirya shi domin samar da hadin kai ga dukkanin bangarorin bayar da agajin gaggawa, ya samu halartar manyan mutane wanda suke da ruwa da tsaki a cikin kungiyar, da kuma wadanda suke bayar da gudummawa a cikin kungiyar, da ma sauran ya'yan kungiyar.

Da farkon taron Sirajo Abba Galadima shi ne ya gabatar da makasudin taron, wanda ya zayyano kalar kalubalen da suke fuskanta na rashin hadin kai ga sauran kungiyoyi, da kuma abubuwan da yakamata su yi, tare da bayyana dalilin da yasa aka kafa ita kanta kungiyar.

Taron ya kara yin nitso a cikin muhimmancin sanin minene ma aikin tun tashi farko, wanda aka bayyana ma mahalarta taron cewa shi dai aikin agaji aiki ne wanda ake yin shi domin Allah, sannan kuma ana yin aikin ne bisa ikilasi, bugu da kari kuma aikin ya ta'allaka ne wajen taimakon al'umma.

Dr Muhammad Auwal, daya daga cikin manyan mutanen da suka halarci taron ya sake jan hankalin ya'yan kungiyar akan muhimmanci aikin, "Komi mutum ke yi ya sanya tsoron Allah a ciki, shi irin wannan aikin, aiki ne da zai baka damar jin tsoron Allah, akwai mutane da suke dogara da kai domin kiyaye lafiyar su, dukiyar su, da sauran abubuwan rayuwar su". Inji shi.

Ya kara da cewa "Ka dauki mutane a matsayin amanar su ce Allah ya dora maka, ka kiyaye masu dukkan abubuwa da suka shafi rayuwar su gwargwadon yadda zaka iya, daga karfe da rufe da cewa "Idan har ka iya yin wannan to shine babban aikin dan agaji.

Hon. Ali Abu Albaba, dan majalissar jiha mai wakiltar karamar hukumar Katsina, kuma daya daga cikin mutanen da aka bayyana su a matsayin masu bada gudunmawa a kungiyar, ya yi jinjina ga kungiyar sannan ya yi mata fatan cigaba da cin nasara a koyaushe, sannan ya tunatar da mahalarta taron muhimmancin hadin kai da kuma muhimmanci aikin agaji a cikin al'umma.

Kungiyar ta karrrama wasu daga cikin wadanda ta kira a matsayin masu taimaka mata, akwai kwamandan Hizba na jihar Katsina, Dr Aminu Usman Abu Ammar, da mataimakin shi,  Malam Ibrahim Iyal Gafai, da Hon. Ali Abu Albaba, da Alhaji Absulaziz Bashir "Khadimul Quran" da sauransu.

Follow Us