Hukumar NDLEA Ta Shirya Taron Fadakarwa Ga Daliban Lafiya a Katsina

top-news

Zaharaddeen Ishaq Abubakar, Katsina Times

Katsina, 29 Yuli 2024 - A ranar Litinin, 29 ga watan Yuli, Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi (NDLEA) ta gudanar da taron fadakarwa na musamman ga ɗaliban kiwon lafiya na makarantar Khuddam da ke Kofar Kaura, Katsina.

Taron ya maida hankali ne kan wayar da ɗaliban game da illolin miyagun kwayoyi da tasirin su ga rayuwar matasa, tare da jan hankali kan yadda za a iya kaucewa amfani da su.

Muhammad Nura Salisu, jami’in hukumar NDLEA a jihar Katsina kuma mai kula da sashen koyarwa da fadakarwa kan illolin kayan maye, ya gabatar da kasidar a madadin hukumar. Ya yi bayani dalla-dalla game da illolin kwayoyi masu ƙarfi da na ruwa, da yadda suke lalata tunani da hankali.

Nura Salisu ya bayyana ire-iren miyagun kwayoyin da yadda suke illatarwa, tare da yadda ake gane masu ta’ammuli da su, da hanyoyin basu shawara don dawowa hayyacinsu, daga matakin fadakarwa har zuwa mika rahoton su ga hukumar don ta dauki mataki.

A cikin kasidar, ya yi bayani kan matakan da hukumar ke dauka na magance matsalolin masu tu’ammuli da kwayoyi, tun daga matakin ajewa a basu masu shaye-shaye kulawa har zuwa matakin shari’a da hukunci ga manyan dillalai.

A zantawarsa da Katsina Times, Nura Salisu ya ce sun zaɓi makarantar lafiya ta Khuddam don gudanar da wannan fadakarwa duba da su malaman lafiya na iya amfani da ilimin su wajen taimakawa mutane kaucewa wannan yanayi ko samar da magungunan da ke da illa ga lafiyar dan’adam.

Ya ce ba makarantar Khuddam kawai ba, shirin zaici gaba kamar yadda suka saba duk shekara na shiga lungu da sako na cikin al’umma don fadakarwa da kara wayar da kan jama’a game da illolin kwayoyi da kuma bayyana matsayar hukumar NDLEA akan masu tu’ammuli da kwayoyin.

Sunan shirin "War Against Drugs Abuse" (WADA), wanda duk inda suka gabatar da kasida suna duba ɗalibai masu hazaka don zama mambobin shirin don su taimakawa hukumar wajen wayar da kai kan illolin miyagun kwayoyi. Taron da aka gudanar a dakin taro na makarantar Khuddam ya samu halartar malaman lafiya daga makarantar da wajen ta irin su Abdulmalik Ibrahim, Nuraddeen Garba, Aliyu Abba, Mr. Oka Okafor, Usman Hassan, Salisu Abdullahi, Madam Aisha, da Babangida Ibrahim, da sauransu.

NNPC Advert