Mukaddashin Gwamna Ya Yaba da Kwalejin Ilimi ta Tarayya Katsina a Taron Yaye Dalibai
- Katsina City News
- 27 Jul, 2024
- 482
Zaharaddeen Ishaq Abubakar, Katsina Times
KATSINA, 27 Yuli 2024 - Barista Abdullahi Garba Faskari, Sakataren Gwamnatin Jihar Katsina, daya wakilci Mukaddashin Gwamna Alhaji Farooq Lawal Jobe a taron hadin gwiwar yaye dalibai na Kwalejin Ilimi ta Tarayya Katsina. Taron, wanda ya hada da bikin yaye dalibai karo na 27 zuwa 43, tare da karrama wasu shahararrun mutane da lambobin yabo na fellowship.
A jawabinsa, Barista Faskari ya mika gaisuwar taya murna daga Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, PhD, CON, ga mahukuntan kwalejin da ma’aikatanta bisa nasarar shirya taron. Ya taya murna ga daliban da aka yaye da kuma shahararrun ‘yan asalin jihar da suka sami lambobin yabo na fellowship, ciki har da Gwamna Radda, Uwargidan Gwamna Hajiya Fatima Shema, Sarkin Katsina Dr. Abdulmuminu Kabir Usman, da Sarkin Daura Alh. Faruk Umar.
Barista Faskari ya jaddada kudirin gwamnati na bai wa ilimi fifiko, wanda ya yi daidai da tsarin manufofin gwamnatin na “Gina Makomar Matasa.” Akwai gyare-gyare da aka yi kwanan nan wanda ya sa Ma’aikatar Ilimi ta koma Ma’aikatar Ilimin Firamare da Sakandare, yayin da Sashen Ilimi Mai Zurfi ya koma cikakkiyar ma’aikata. Wadannan canje-canjen na da nufin kara daukaka harkar ilimi a jihar. Ya bayyana
Yayin da yake bayyana nasarorin da gwamnatin ta samu a shekarar da ta gabata, Barrister Faskari ya bayyana daukar fiye da malamai dubu bakwai aiki, ciki har da masu kwallayen kwalejin fiye da dubu hudu. Ya kuma ambaci biyan kudaden fara aikin gina sababbin makarantun sakandare 75 a karkashin shirin AGILE, wanda ya kai naira biliyan 5.68. Bugu da kari, gwamnatin jiha ta rage wa iyaye nauyin kudi ta hanyar biyan kudaden jarabawa na WAEC, NECO, NBAIS, da NAPTEB, wanda ya kai naira biliyan 1.39, da kuma biyan bashin da aka rika na naira miliyan 177 na kudaden jarabawar NECO.
Haka kuma, jiha ta ware naira biliyan 3.2 a matsayin tallafin karatu ga dalibai 260,899 da suke ci gaba da kuma sabbin daliban manyan makarantu daga shekarar karatu ta 2017 zuwa 2023.
Faskari ya yi kira ga daliban da aka yaye su yi amfani da horon da suka samu wajen kare martabar ilimi. Ya kammala da gode wa mahukuntan kwalejin saboda karrama shahararrun mutane da lambobin yabo na fellowship tare da taya murna ga wadanda suka sami lambobin yabo a madadin gwamnati da jama'ar Jihar Katsina.