Zaharaddeen Ishaq Abubakar | Katsina Times
Gwamnatin Jihar Katsina ta ɗauki matakin farfaɗo da tsarin ilimin manya da na zamani a fadin jihar, da nufin dawo da martabar ilimi da samar da damammaki ga al’umma musamman mata da mutanen da suka wuce shekarun makaranta.
A karkashin jagorancin Hajiya Bilkisu Muhammad Kaikai, Babbar Sakatariya a Hukumar Kula da Ilimin Manya ta Jihar Katsina (Katsina State Agency for Mass Education), gwamnatin ta sake bude Ajin karatun manya a zaurukan hakimai 68 da ke masarautun Katsina da Daura, inda ake koyar da karatu da sana’o’i domin taimaka wa mutane su dogara da kansu.
Ajin Manya na nufin samar da dama ga duk wanda bai samu damar kammala karatu ba a lokacin da ya dace, ko kuma waɗanda basu taba zuwa makaranta ba. A sabon tsarin da gwamnatin jihar ta dawo da shi, an ware gurabe a kowace gundumar hakimmi (Sarakunan gargajiya) domin bai wa jama’a dama su koyi karatu, rubutu da kuma sana’o’in hannu da za su iya amfani da su domin habaka tattalin arzikin kansu da na al’umma.
Hajiya Bilkisu Kaikai ta bayyana cewa, “Ba wai ilimi kawai muke koyarwa ba, har da sana’o’in hannu domin dogaro da kai ga wadanda suka je makarantun
Ta ƙara da cewa, yawancin masu halartar ajin Dattawa ne, wanda hakan ke nuna yadda jama’a ke fahimtar muhimmancin ilimi. “Komai tsufan mutum, yana zuwa makaranta kuma yana fahimta,” in ji ta.
Don tabbatar da inganci da tsarin, hukumar karkashin jagorancin Hajiya Bilkisu ta gudanar da rangadi a shiyyoyi hudu na jihar: Katsina, Daura, Funtua da Dutsinma, domin tantance takardun malamai da tabbatar da ingancin koyarwar da ake bayarwa a wuraren.
Haka kuma an ci gaba da bai wa malamai horo na musamman domin inganta dabarunsu da sabbin hanyoyin koyarwa, tare da ƙirƙiro sashin da ke kula da masu bukata ta musamman, domin tabbatar da cewa kowa yana da damar samun ilimi ba tare da wani shinge ba.
A watannin baya, Hajiya Bilkisu Kaikai ta kai ziyara ga sarakunan gargajiya na masarautun Katsina da Daura domin bayyana kudirin gwamnatin malam Dikko Umar Radda, Sarakunan sun nuna goyon baya 100%, inda suka ce wannan tsari tsoho ne da tun da dadewa masarautun ke sa ido da nuna sha’awa a kai.
A yayin ziyarar, an raba kayan koyarwa da koyo domin ƙarfafa cigaban shirin, tare da tabbatar da cewa makarantu sun samu kayan aiki da suka dace.
A wani sabon salo da ke ƙara ƙarfin tsarin ilimi a jihar, hukumar hadin gwiwa da babban dakin karatu na kasa shiyyar Katsina, ta shirya wani shiri mai taken Digital Literacy Program (Learning by Radio), wanda ke koyar da ilimin zamani ta hanyar rediyo.
Don horar da malamai kan yadda za su gabatar da darussa ta hanyar murya kawai, ba tare da gani da ido ba, a taron da aka gudanar ranar Litinin a Dakin Taro na Babban Dakin karatun na Kasa, reshen Katsina.
Shirin ya samu goyon bayan Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya, inda malamai suka koyi dabaru na tsara darussa da yadda za su ja hankalin dalibai ta hanyar amfani da rediyo.
Taron ya bada damar bude wata sabuwar hanyar koyarwa, kuma ya sa su fahimci muhimmancin rediyo wajen yada ilimi a yankunan da babu isassun makarantu.
An tsara cewa wannan horo da tsarin rediyo zai ci gaba tare da ƙarin shirye-shirye na amfani da fasahar zamani wajen yada ilimi. Wannan wani ɓangare ne na yunkurin gwamnatin Katsina da hadin gwiwa da tarayya domin tabbatar da cewa ba wanda ya rage baya a fannin ilimi, musamman a arewacin Najeriya.
Wannan tsari na zamani da na ilimin manya yana da muhimmiyar rawa wajen rage jahilci da haɓaka wayar da kan jama’a, tare da inganta rayuwar mata da sauran al’umma a jihar Katsina.