Katsina Ta Samu Nasara Wajen Rage Ta'ammali da Miyagun Kwayoyi -NDLEA
- Katsina City News
- 26 Jul, 2024
- 368
Zaharaddeen Ishaq Abubakar, Katsina Times
Barista Abdullahi Garba Faskari Sakataren Gwamnatin jihar Katsina
Jihar Katsina ta samu gagarumar nasara wajen rage yawan masu ta'ammali da miyagun kwayoyi, inda ta koma ta shida a jerin jihohin da ke fama da wannan matsala, sabanin shekarar da ta gabata inda ta kasance ta biyu.
Shugaban Hukumar Hana Sha da Fatauci da Miyagun Kwayoyi ta Kasa (NDLEA) reshen jihar Katsina, Hassan Sani Abubakar, ne ya bayyana wannan nasara lokacin da tawagar hukumar ta kai ziyarar bangirma a ofishin Sakataren Gwamnatin jihar Katsina ranar Juma'a, 26 ga watan Yuni 2024, don bayyana nasarorin da suka samu a cikin shekara guda.
Hassan ya sanar da gwamnatin jihar Katsina cewa, "A shekarar da ta gabata, mun kawo muku rahoton cewa Katsina ta kasance ta biyu a jerin jihohin da ke fama da ta'ammali da miyagun kwayoyi. A yau, muna farin cikin sanar da ku cewa mun samu gagarumar nasara inda yanzu Katsina ta koma ta shida." Ya kara da cewa, "A kasa da watanni biyu, mun kama miyagun kwayoyi masu nauyin kilogram 900 a jihar Katsina, wanda wannan ba karamar nasara bace."
Shugaban NDLEA a jihar Katsina ya bayyana bukatar su na karin goyon bayan gwamnatin jihar wajen samar musu da kayan aiki don kara musu karfin gwiwa da damar zagaye duk fadin jihar domin dakile wannan barna. Ya ce, "A da bamu da isassun ma'aikata, amma yanzu muna da ma'aikata. Muna bukatar karin motoci daga gwamnati, domin yanzu muna da motoci biyu kawai."
Haka kuma, hukumar ta nemi goyon bayan gwamnatin jihar Katsina wajen shirya tarurrukan kara wayar da kai da za su hada kai da wasu bangarori na hukumomin jihar, da kuma izini na zuwa makarantun sakandare da na gaba da sakandare don gwajin kwayoyi ga dalibai.
A nasa jawabin a madadin gwamnatin jihar Katsina, Sakataren Gwamnatin jihar, Barista Abdullahi Garba Faskari, ya yaba matuka da irin wannan gagarumin ci gaba da hukumar ta NDLEA ta samu. Faskari ya tabbatar da cikakken goyon bayan gwamnatin jihar Katsina ga wannan yunkuri na hukumar NDLEA, inda ya bayyana cewa, tushen ta'addancin da jihar ke fama da shi shine shan miyagun kwayoyi. Don haka ya ce za a duba dukkan bukatunsu, kuma za a aiwatar da su, saboda wannan na daya daga cikin kudirorin da gwamnatin jihar Katsina karkashin jagorancin Malam Dikko Umar Radda ta bawa muhimmanci.
Taron ya samu halartar sakatarori da daraktocin gwamnatin jihar Katsina a ofishin Sakataren Gwamnatin jiha tare da tawagar bangarorin tsaro na hukumar NDLEA reshen jihar Katsina.