Sasanci Tsakanin 'Yan Takara: Shugaban NULGE Jihar Katsina Ya Bayyana Muhimmancin Sulhu
- Katsina City News
- 23 Jul, 2024
- 367
23-7-24. NULGE/Musawa/Matazu.
Shugaban Kungiyar Ma'aikatan Kananan hukumomi ta kasa reshen jihar katsina Comrade Nasiru Wada Maiadua Dan Saran Daura ya bayyana sasanci a tsakanin yan takara da cewa mataki ne na tafiya da kowa tare da kara samun fahimtar juna .
Shugaban kungiyar ta NULGE ya bayyana hakan ne jim kadan bayan karban rantsuwa da sabbin zababbun shugabannin kungiyar na Kananan hukumomin Musawa da Matazu da ke shiyyar Funtua su ka yi .
Shugaban kungiyar na jihar katsina Comrade Nasiru Wada Maiadua Dan Saran Daura wanda ya kara jaddada muhimmancin yin sulhu a tsakanin yan takara ya yi dogon jawabi dangane da nasarorin da kungiyar ta samu wanda ya hada da zuwa matakin albashi na 16 wanda a cewar shi ba karamar nasara ba ce.
Ya kuma jaddada godiyar shi ga ga Gwamnan jihar katsina Malan Dikko Umaru Raddah da Yan majalisar dokoki ta jihar katsina da hukumar kula da karin girma Da'a da Ladabtar da Ma'aikatan Kananan hukumomi ,shugabannin Kananan hukumomin Musawa da Matazu Dr Habibu Abdulkadir da Kwamared Shamsudden Muhammad Sayaya wanda ya taba zama shugaban kungiyar a karamar hukumar Matazu bisa goyon baya da hadin kai da su ke ba yayan kungiyar ta NULGE.
Dan Saran Daura daga nan sai ya bukaci ganin sabbin zababbun shugabancin su na gudanar da salon mulkin su na barin kofa a bude domin saurarron yayan kungiyar da su ka ba su amana , ya na mai cewa yin hakan zai ba su damar barin tarihi na ayyukan ci gaba a karshen shugabancin su.
A na shi jawabin Dan majalisa mai wakiltar karamar hukumar Musawa a majalisar dokoki ta jihar katsina kuma shugaban kasafin kudi Alhaji Lawal Yaro ya bayyana kungiyar ma'aikatan Kananan hukumomi ta kasa reshen jihar katsina a matsayin ginshiki wadda ta dace da shugaba kuma jagora ya kara da cewa kungiyar NULGE ta fi kusa da kowace kungiya .
Honourable Lawal daga nan sai ya kara bayar da tabbacin ci gaba da bayar da goyon bayan majalisar dokoki ta jihar katsina da ke kalkashin jagorancin Rt Hon Nasiru Yahya Daura .
Tun farko a na shi jawabin shugaban karamar hukumar Musawa Dr. Habibu Abdulkadir ya bayyana kungiyar NULGE ta Karamar hukumar a matsayin tsintsiya madaurin ki daya .
Haka shi ma takwaran shi na Karamar hukumar Matazu Kwamared Shamsudden Muhammad Sayaya ya kara bayar da tabbacin ci gaba da bayar da goyon baya da hadin kai ga sabbin zababbun shugabannin kungiyar NULGE na Karamar hukumar Matazu .
A jawaban su daban daban na karban jagorancin kungiyar NULGE shugaban kungiyar na karamar hukumar Musawa Kwamared Mustafa Abdulmumini da na Karamar hukumar Matazu Kwamade Yushau Ibrahim godiya su ka yi ga shugabannin Kananan hukumomin su da kungiyar NULGE a matakin jiha da na yankunan su dangane da goyon baya da hadin kai da a ke ba su .
Dukkan su sun bayar da tabbaci na gudanar da kyakkyawan shugaban ci.
Daga karshe kungiyar NULGE ta jiha ta bayar da lambar girmamawa ga shugaban karamar hukumar Matazu daga baya a ka ba shugaban kungiyar NULGE ta jiha Comrade Nasiru Wada Maiadua.
Haka kuma kungiyar NULGE ta bayar da lambar girma ga Dan Majalisar dokoki mai wakiltar Karamar hukumar Musawa Honourable Lawal Yaro
Kadan daga cikin wadanda su ka raka shugaban kungiyar ta NULGE na jihar katsina sun hada da Mataimakin shi Comrade Abdulhadi Sani Kankara ,Sakatare Comrade Kolo Maigana,da Sakataren walwalar kungiya Comrade Aminu Shantali ,Sakataren yada labarai kwamared Nura Rabiu Dabai da Matashin Kungiyar Kwamade Nura Dan Shehu Matazu da Akawun kungiyar Comrade Kabir Yahya da Comrade Ashiru Mamman da sauran su.
COV. Sadiq