Kwamitin Bincike ya Ƙwace Filayen Daji na Jibiya da Aka Mallaka Ba Bisa Ka'ida Ba
- Katsina City News
- 21 Jul, 2024
- 373
Kwamitin binciken gandun daji a ƙarƙashin jagorancin Alhaji Khalil Baƙo ya gudanar da samame da bincike a dazukan ƙaramar hukumar Jibiya.
Gwamnan jihar Katsina, Malam Dikko Raɗda, ya ƙaddamar da kwamitin domin ƙwato dukkanin filayen daji da aka mallaka ba bisa ka'ida ba a faɗin jihar daga shekarar 2017 zuwa 2023.
Kwamitin ya zagaya dazuka mallakin gwamnati a dukkanin kananan hukumomi 34 dake faɗin jihar. Dazukan da kwamitin ya ziyarta sun haɗa da dajin Ɗaɗɗara da Ginzo duk a ƙaramar hukumar Jibiya.
Shugaban kwamitin ya sha alwashin rubuta cikakken rahoto da zai bai wa Gwamnan jihar Katsina.