Ma’aikatar Lafiya da Ma’aikatar Kasafin Kudi ta Jihar Katsina Sun Shirya Taron Bita Akan Abinci Mai Gina Jiki a Jihar Kano
- Katsina City News
- 20 Jul, 2024
- 535
Ma’aikatar Lafiya hadin Gwiwa da Ma’aikatar Kasafin Kudi ta Jihar Katsina sun Shirya Taron Bita na Masu Ruwa da Tsaki a kan Abinchi Mai Gina Jiki a Jihar Kano
Shirin inganta sakamakon abinci mai gina jiki a Nijeriya (ARiN) dake Ma’aikatar Lafiya ta Jihar Katsina hadin gwiwa da Ma’aikatar Kasafin Kudi da tsare-tsare ta Jihar Katsina sun shirya tattaunawa ta musamman da masu ruwa da tsaki da suka hada da Majalisar Jihar Katsina, Kungiyar Shugabannin Kananan Hukumomi ta Jihar Katsina domin wayar da kai Akan muhimmancin sa lamurran abinci mai Gina jiki a kasafin kudin kananan Hukumomi na Jihar Katsina.
Taron ya gudana a Bristol Hotel dake Jihar Kano a ranar Juma’a, 19 ga watan Juli 2024.
Kakakin Majalisar Dokoki ta Jihar Katsina, Rt. Hon. Nasir Yahya Daura, a lokacin da yake jawabin bude taron kara ma juna sani, ya tabbatar da cewa majalisar dokokin jihar Katsina ta himmatu wajen tallafa wa hukumomin gwamnati da abokan huldar ci gaba wajen inganta rayuwar al’ummarmu.
A cewar shi, “Mun fahimci mahimmancin abinci mai gina jiki don haɓaka rayuwar al'ummarmu, musamman yara da mata. Ina yabawa ofishin ANRiN da ma'aikatar kasafin kudi da tsare-tsare ta tattalin arziki bisa kokarinsu na shirya wannan taron bita.”
Shi ma a nashi jawabin, Kwamishinan kasafin kudi da tsare-tsare ta tattalin arziki na Jihar Katsina, Hon. Bello Kagara, ya bayyana amfanin abinci mai gina jiki ga kananan yara Wanda ya shaida cewa Gwamnatin Jihar Katsina tun daga kafuwar ta, ta bada gudunmuwa wajen ganin an samu cigaba a wannan fannin.
Shugaban Shirin ARiN ta Jihar Katsina, Dr. Umar Bello, a lokacin da yake jawabi ya bayyana Makasudin taron bitar domin Kara ma juna sani da kuma wayar da Kai ga masu ruwa da tsaki musamman Shugabannin Kananan Hukumomi na Jihar Katsina akan mahimmancin ware kaso mai tsoka akan abinchi mai gina jiki a cikin kasafin kudi na Kananan Hukumomi domin muhimmancin shi ga yara masu kananan shekaru.
Ya shaida cewa wannan shiri na ARiN yana da Manufar ƙara yawan amfani da ingantaccen abinci mai gina jiki mai nagarta ga mata masu juna biyu da masu shayarwa. Ya bayyana cewa kananan hukumomi 18 a Katsina da suka kunshi cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko 188 a halin yanzu suna cin gajiyar shirin.
Wasu daga cikin ayyukan da shirin ke badawa sun hada da samar da sinadarin Vitamin A ga yara ‘yan kasa da shekaru biyar, Ion polic acid ga mata masu juna biyu, ORS acid don rigakafin gudawa da dai sauransu.
Wadanda suka bada gudunmuwa wajen tattaunawa a taron bitar sun hada Kwamishinan Ma’aikatar Kananan Hukumomi ta Jihar Katsina, Farfesa Badamasi Charanchi, wakilin Kungiyoyin Sa Kai, Shugaban Kwamitin Kasafin Kudi na Majalisar Jihar Katsina, Hon. Lawal Jikamshi da sauran su.
Majalisar Dokokin Jihar Katsina a lokacin bitar ta bada tabbacin cewa zata bada duk wata gudunmuwa wajen yin doka da zata inganta al’amarin abinchi mai gina jiki a kananan yara a Jihar Katsina.