Faruq Lawal Jobe Ya Karbi Baƙi a karon farko matsayin Gwamnan riƙo na jihar Katsina
- Katsina City News
- 19 Jul, 2024
- 372
A matsayinsa na mukaddashin gwamnan jihar Katsina, Malam Faruk Lawal Joɓe, ya karbi baƙuncin Dr. Ahmed Hamza, sakataren dindindin na ma’aikatar lafiya, tare da wata tawaga daga Faculty of Family Medicine na National Postgraduate Medical College of Nigeria.
Mukaddashin gwamnan ya gode wa Dr. Hamza da tawagarsa kan yabo da goyon bayan da suka nuna wa bangaren lafiya na jihar. Ya jaddada cewa gwamnati ta bunƙasa wasu muhimman Ayyuka da suka shafi bangaren lafiya daga asibitocin farko har zuwa na gaba. Hakan ya sa jihar Katsina ta zama ta daya wajen yawan cibiyoyin kiwon lafiya na farko a ƙasar.
Ya bayyana cewa gwamnatin jihar ta haɓaka kuma ta sauya cibiyoyin kiwon lafiya na farko guda hudu zuwa Manyan Asibitoci.
Mukaddashin gwamnan ya kara da cewa, “A fahimtar bukatar ƙarin likitoci, gwamnatin jihar ta dauki nauyin dalibai 41 zuwa ƙasar Masar don yin karatun likitanci.”
Har ila yau, ya bayyana cewa gwamnatin jihar ta amince da daukar ƙarin ma’aikatan jinya da lafiyar don cike gibin da ake da shi. Cikin shekara guda, gwamnatin jihar ta gina cibiyar yin jinyar koda ta zamani, mafi inganci a ƙasar, da nufin mayar da Katsina cibiyar yawon buɗe ido a bangaren kiwon lafiya.