Gwamnan Kano Ya Naɗa Sabbin Sarakunan Rano, Karaye, Da Gaya
- Katsina City News
- 17 Jul, 2024
- 571
Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano ya amince da nadin sabbin sarakunan Rano, Gaya da Karaye masu daraja ta uku.
Sanarwar da mai magana da yawun gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar kuma ya rabawa manema labarai a Kano ta ce sabbin masarautun za su kasance a matsayi na biyu, tare da masarautar Kano a matsayin ta farko.
Sabbin sarakunan da aka nada sune:
1. Alhaji Muhammad Mahraz Karaye- Sarkin Karaye (a da, Hakimin Rogo).
2. Alhaji Muhammad Isa Umar - Sarkin Rano (a da, Hakimin Bunkure).
3. Alhaji Aliyu Ibrahim Abdulkadir Gaya - Sarkin Gaya (a da, Sarkin rusasshiyar masarautar Gaya).
Gwamna Abba Kabir Yusuf, yayin taya sabbin Sarakunan murna, ya umarce su da su kasance masu kula da al’adu, zaman lafiya, da hadin kan al’ummar masarautunsu.
A ranar Talata, 16 ga Yuli, 2024, Gwamnan ya rattaba hannu kan kafa masarautu masu daraja ta biyu a jihar. Masarautar Rano za ta kunshi kananan hukumomin Rano, Kibiya, da Bunkure; masarautar Gaya za ta hada da kananan hukumomin Gaya, Ajingi, da Albasu; yayin da masarautar Karaye za ta kunshi kananan hukumomin Karaye da Rogo.