TARIHIN GIDAN YARIMA, KATSINA
- Katsina City News
- 13 Jul, 2024
- 655
GIDAN YARIMA. KATSINA
Gidan Yarima Sarkin Katsina Ibrahim Dan Bello ne ya Gina shi acikin shekarar 1870, ya Gina wannan gidanne yaba danshi Yarima Abubakar, lokacin shi Abubakar Yana Yarima kamin ya zama Sarkin Katsina a shekarar 1887. Babban gidane Wanda yake a Unguwar Yarima, Gidan Yana tsakanin Unguwar Alkali da Sararin Kuka a Birnin Katsina.
Ada baya ga Gidan Korau, watau Gidan Sarkin Katsina babu wani gida na kasaita a Katsina kamar Gidan Yarima. An kirashi da Gidan Yarima saboda Yariman Katsina Abubakar ya fara zama Gidan, a duk lokacin da yazo Katsina daga Safana to Gidan Yarima yake sabka.
Ita dai wannan Sarautar ta YARIMA, tsohuwar Sarautace domin Tarihi ya nuna tun lokacin da Muhammad Korau ya kawo tsarin Sarautu a Katsina, to akwai wannan Sarautar Kuma babban Dan Sarki ake ba ita wannan Sarautar, kalmar Yariman ma abinda take nufi kenan watau babban Dan Sarki Mai Jiran Gado. Mutum na farko daya fara Sarautar Yarima a lokacin Habe shine Usman Maje Dan Sarkin Katsina Muhammadu Korau (1348-1398). A lokacin da Ummarun Dallaje ya zama Sarkin Katsina Sai ya nada babban Dan shi watau Muhammad Bello a matsayin Yariman Katsina. Har ya zuwa yanzu Dallazawa sune suke rike da wannan Sarautar ta YARIMA.
Shi wannan Gida na Yarima Tarihi ya nuna lokacin da Turawan Mulkin Mallaka suka zo Katsina acikin shekarar 1903, a Gidan Yarima ne aka fara sabka dasu, domin a wannan lokacin kamar yadda bayani ya gabata baya ga Gidan Korau babu wani na kasaita kamar Gidan Yarima.
Turawan Ingila sun biyo ta Kofar Yandakane, Amma baayi fada dasu bu, an yi yarjejeniya dasu a Gidan Yarima, Wanda asabili da hakane suka sake nada Sarki Abubakar aka bashi Sandar Girma ta Ingila, wannan ya nuna cewa umarnin Sarki ya tashi daga Sarkin Musulmi a Sokoto ya koma ga Rasdan da Gwamna na Turawa. Haka akayi ta tafiya har takai ga daga baya Turawa sun Cire Sarki Abubakar a shekarar 1905 aka ba Kanen Mahaifinshi watau Malam Yero, shima Yeron acikin shekarar 1906 aka cire shi, aka ba Durbin Katsina Muhamnad Dikko Sarkin Katsina. Wannan shine ya kawo karshen mulkin Fulani Dallazawa, ya koma hannun Fulani Sullubawa.
Alhaji Musa Gambo Kofar soro.