GIDAN KORAU: KOFAR SORO KATSINA
- Katsina City News
- 12 Jul, 2024
- 373
GIDAN KORAU.
Gidan Korau, shine Gidan Sarautar Katsina na yanzu, Yana a tsakiyar Birnin Katsina. Kamar yadda Marubuta Tarihi irinsu Dr. Yusuf Bala Usman, Hogaben S. J. suka rubuta, an Gina Gidan Korau a shekarar 1348, Wanda Sarkin Katsina Muhammadu Korau ya Gina. Muhammadu Korau kamar yadda sunan shi ya nuna shine Sarkin Katsina Musulmi na farko, wannan dalilin ne yasa har ya zuwa yanzu ake Kiran da sunan Gidan Korau. Gidan Yana daya daga cikin tsofafin Gina gine a Fada a Kasar Hausa, sauran sune Daura, Kano da Zazzau.
An zagaye Gidan Korau da Ganuwa, wadda ake cema Ganuwar Gidan Korau, Kuma an yima ma Gidan Kofofi biyu, watau Kofar Soro wadda ake bi a shiga Gidan Korau, Sai Kofar Bai wadda ke bayan Gidan Korau. Ita Kofar Bai tana a matsayin Kofar sirri a wancan Lokacin ( Secret door) Sarki Yana fita ta Kofar akan wata fita ta bazata, Sarkin Bai shine yake kula da Kofar Bai, sauran ayyukan Sarkin Bai sun haka da Ajiye bayin Sarki da kula dasu, da Kuma nemoma Sarki bayi.
An Gina Gidan Korau akan kayan gini irin na Gargajiya kamar Tubali, Kwababiyar Kasa, Kyami da sauran kayan gini na Gargajiya irinsu Asabari, Jangargari, Makuba da sauransu.
Daga cikin farfajiyar Gidan Korau akwai kananan Unguwanni Wanda yawancin su mutanen fada ne suke zaune aciki kamar Tsamiya, Garjagau, Unguwar Kuka, Unguwar Gadi, Tabkin Lambu da sauransu. A Unguwar Tsamiyane Makabartar Dallazawa take inda aka rufe Sarkin Katsina Malam Ummarun Dallaje da wasu sauran Sarakunan Dallazawa, da Galadiman Katsina Dudi. Ita Kuma Garjagau mafi yawan Mazaunan ta Badawane zuruar Turaki Agawa. Unguwar Kuka nanne suke da Sarautar Ajiya, watau Ajiya Miya, Ajiya Danladi, Ajiya Abubakar da sauransu, a Unguwar Kukanne Kuma akayi Sarautar Sarkin Gandu. Tabkin Lambu nanne Makabartar Sarakunan Musulunci na Sullubawa take inda aka rufe Sarkin Katsina Muhammadu Dikko, da Dansa Sir Usman Nagogo da Sarkin Katsina Muhammadu Kabir.
A dai cikin Gidan Korau din aka Gina Baitil Mali na farko na Arewacin Nigeria ( First Treasury). Wanda aka Gina a shekarar 1908 a lokacin mulkin Sarkin Katsina Muhammadu Dikko. Akwai babban Dakin adana Kofuna na Polo da suka acikin Gidan Korau Wanda ake cema Dakin Cup, domin Katsina tana da babban Tarihi na wasan Dawaki a Nigeria, Sarkin Katsina Alhaji Sir Usman Nagogo shine Zakaran Farko na wasan Polo a Nigeria Yana da Handcap +7.
Musa Gambo Kofar soro.
(12-07-2024)