Gwamnatin Katsina Ta Sha Alwashin Saukaka Hanyoyin Kasuwanci da Taimakawa Masu Zuba Jari
- Katsina City News
- 11 Jul, 2024
- 513
Maryam Jamilu Gambo, Katsina Times
Gwamnatin jihar Katsina ta kudiri aniyar saukaka hanyoyin kasuwanci da samar da cikakken goyon baya ga masu zuba jari a jihar.
Gwamna Dikko Umaru Radda ya bayar da wannan tabbaci yayin da ya karbi bakuncin Sakatariyar Zartarwa ta Hukumar Kula da Zuba Jari ta Najeriya (NIPC), Hajiya Aisha Rimi, a lokacin wata ziyara ta ban girma a gidan gwamnati.
Tun bayan karbar ragamar mulki a shekarar 2023, gwamnatin Radda ta mayar da hankali wajen samar da yanayi mai kyau ga kasuwanci don jan hankalin masu zuba jari. "Muna aiki tukuru wajen saukaka takunkumi da ba wa masu zuba jari goyon bayan da suke bukata don cimma nasara," in ji shi.
Gwamna Radda ya jaddada muhimmancin biyan bukatun masu zuba jari cikin lokaci da inganci. "Abin da muka fi baiwa muhimmanci shi ne cika bukatun masu zuba jari cikin gaggawa," ya ce.
Ya kara da cewa wannan aniyar tana bayyana a cikin kokarin gwamnatin na sarrafa ayyukan gwamnati ta hanyar fasaha, don samar da gaskiya da rikon amana. Gwamnan ya bayyana wasu tsare-tsare irin su Asusun Bai-daya na Gwamnati (TSA), tara kudaden shiga ta hanyar fasaha, da wani shafin yanar gizo da za a kaddamar a watan Agusta a matsayin wani bangare na kokarin gwamnati don samar da gaskiya a cikin kudaden shiga da fita.
Gwamna Radda ya kuma bayyana kafa hukumar kula da ci gaban jihar ta musamman. Wannan hukuma za ta kula da kuma sa ido kan ayyukan da suka shafi ci gaba, kungiyoyi masu zaman kansu (NGOs), da sauran kungiyoyi da ke aiki a cikin jihar, don tabbatar da cewa dukkanin ayyuka sun bi tsari kuma an kammala su cikin lokaci.
Wani muhimmin tsari da gwamna Radda ya bayyana a wajen taron shi ne Rukunin Tsare-tsare da Kulawa, wanda ke aiki kai tsaye karkashin ofishin Gwamna. Wannan rukunin na da muhimmiyar rawa wajen tabbatar da cewa an kula da kuma auna dukkanin tsare-tsaren gwamnati yadda ya kamata.
Tun da farko, Sakatariyar Zartarwa ta NIPC, Hajiya Aisha Rimi, ta bayyana burin hukumar na taimakawa masu zuba jari a Najeriya, duka wadanda ke shigowa kasuwa da wadanda suka riga suka kafa kasuwancin su. Ta ce wani muhimmin bangare na aikinsu shi ne karfafa masu zuba jari su tuntubi hukumomin zuba jari na jihohi.
NIPC na gudanar da ziyara jihohi, suna ganawa da gwamnonin jihohi, hukumomin zuba jari, da kuma masu zuba jari. A cewarta, wannan hanya tana ba su damar samun bayanai kai tsaye kan ayyukan jihohi da kalubale, wanda zai basu damar ba da taimako wanda ya dace.
NIPC na ziyara a jihohin arewa maso yamma, ciki hadda jihar Katsina.
Ta roki Gwamnan Katsina, wanda shi ne Shugaban Kungiyar Gwamnonin Arewa Maso Yamma, da ya jagoranci ingantacciyar hadin gwiwa tsakanin gwamnonin jihohi da NIPC, don kara saukaka hanyoyin zuba jari a fadin yankin.