- GWAMNATIN ZAMFARA TA BADA UMURNIN ƊAUKAR 'YAN SA-KAI

top-news

DAGA TARON MAJALISAR ZARTASWA

- GWAMNATIN ZAMFARA TA BADA UMURNIN ƊAUKAR 'YAN SA-KAI 

- ZA TA GINA TARE DA SABUNTA AZUZUWA SAMA DA 200

A jiya Litinin ne gwamna Dauda Lawal ya bayar da umurnin ɗaukar 'yan sa-kai a matsayin ƙari ga ƙoƙarin da jami'an tsaro ke yi don magance matsalar tsaro. 

Ɗaukar 'yan sa-kai na ɗaya daga cikin muhimman abubuwan da aka tattauna a zaman majalisar zartaswar jihar Zamfara, wanda Gwamna Lawal ɗin ya jagoranta.

Wata sanarwar da mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman Bala Idris ya fitar, ta ce an gudanar da wannan zama na majalisar zartaswar ne a fadar gwamnatin jihar dake Gusau. 

Ya ƙara da cewa, har wayau, a wurin taron majalisar ta bada umurnin a gina sabbin azuzuwan karatu, tare da sabunta wasu a faɗin ƙananan hukumomi 14 na Jihar. 

Ya ce: "A yunƙurinsa na ganin an kawo ƙarshen matsalar tsaro, Gwamna Dauda Lawal ya aminta da ɗaukar 'yan sa-kai a dukkanin ƙananan hukumomin Zamfara. 

"Duk dai a zaman majalisar zartaswar da ya jagoranta, ya aminta da ginawa, tare da sabunta azuzuwan karatu a faɗin ƙananan hukumomin. 

"Za a ɗauki 'yan sa-kai 300 a kowacce ƙaramar hukuma ta jihar. Waɗanda za a basu horaswar da ta dace, domin su ci gaba da taimakawa soji da 'yan sanda kan yaƙi da 'yan ta'adda. 

"Majalisar ta aminta da gina sabbi tare da sabunta azuzuwan karatu guda 49 a Gusau, 11 a Anka, 15 a Bakura, 8 a Bukkuyum, 14 a Birnin Magaji, 8 a Bungudu, 8 a Gummi, 19 a Kauran Namoda, 8 a Maru, 11 a Maradun, 42 a Shinkafi, 8 a Talata Mafara, 27 a Tsafe da kuma guda 11 a Zurmi."

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *