Gwamna Dikko Umaru Radda na Jihar Katsina Ya Nemi Hadin Gwiwa Don Faɗaɗa Shirin Ciyar da Dalibai a Makarantun Firamare
- Katsina City News
- 10 Jul, 2024
- 464
Maryam Jamilu Gambo, Katsina Times
Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, ya gabatar da bukatar hadin gwiwar ƙasa da ƙarin kuɗi don tallafa wa faɗaɗa shirin ciyar da dalibai a makarantun firamare na gida a Najeriya.
Ya bayyana haka ne bisa la’akari da tasirin shirin a fannin zamantakewa da tattalin arziki da kuma damar da yake da ita wajen rage yawan yaran da ba sa zuwa makaranta tare da ci gaba da karatunsu har su kammala.
Gwamnan ya yi wannan kiran ne yayin da yake karɓar bakuncin Kwamishiniyar Kula da Shirin Ciyar da Dalibai na Gida na, ta Gwamnatin tarayya, Injiniya Hajiya Anjor Obande, a wata ziyarar ban girma.
Gwamna Radda ya kuma ba da shawarar a yi amfani da kuɗaɗen da Hukumar EFCC ta kwato wajen tallafa wa shirin.
Yayin da yake jaddada nauyin kuɗin da jihar ke ɗauka, Gwamna Radda ya nuna cewa gwamnatin jihar tana kula da ciyar da sama da ɗalibai 30,000 a makarantun kwana, tare da sauran ayyuka da shirye-shirye. Ya kara da cewa, lamarin ya ƙara ta’azzara saboda batun ƙarin mafi ƙarancin albashi da ke jiran a warware.
Duk da haka, ya jaddada cewa faɗaɗa shirin ciyar da ɗalibai a Jihar Katsina don haɗa ɗalibai kusan miliyan biyu daga aji ɗaya zuwa na uku zai ƙara yawan masu amfana. Ya tabbatar da cewa gwamnatinsa ta shirya tsaf don tallafa wa aiwatar da shirin yadda ya kamata.
A jawabin ta Kwamishiniyar shirin, Injiniya Hajiya Anjor Obande, ta bayyana cewa shirin ciyar da dalibai na gida wanda gwamnatin da ta gabata ta ƙaddamar an dakatar da shi a watan Fabrairu saboda wasu matsalolin da aka gano.
Duk da haka, ta tabbatar da cewa an dawo da shirin tare da nufin ƙirƙirar babban tasiri. Hajiya Obande ta lura cewa shirin yana tabbatar da cewa ɗaliban makaranta suna samun abinci mai gina jiki, wanda ke haɓaka sakamakon karatu da kuma ƙarfafa su don kammala karatunsu.
Ta bayyana cewa gwamnatin tarayya za ta faɗaɗa shirin daga yara miliyan goma da aka fara da su zuwa miliyan goma sha biyar. Ta ce nufin shine a haɗa yara daga aji huɗu zuwa na shida.
Hajiya Obande ta yi kira da a kara haɗin gwiwa da gwamnatocin jihohi don tabbatar da nasarar shirin.
Tun da farko, Dr. Mudasir Nasir, Kwamishinan Kula da Shirin na Ƙasa kuma Babban Darakta, ya bayyana cewa Jihar Katsina tana da tsarin manufofi da goyon bayan da za su tabbatar da ci gaba da aiwatar da shirin a jihar.