KWALEJIN KATSINA ( KATSINA COLLEGE 1922).
- Katsina City News
- 10 Jul, 2024
- 358
An bude babbar Kwalejin ilimi tarko a Arewacin Nigeriya a Katsina acikin shekarar 1922. Kamar yadda Babban Gwamna Nigeriya na lokacin yayi jawabi wajen bude Makarantar, babban dalilin da yasa aka bude Training College a Katsina shine Katsina ta taba kasancewa babbar cibiyar center ta koyar da ilimin addini tun kamin zuwan Bature, dalilii na biyu shine Kasar Katsina ta taba zama babbar cibiyar Kasuwanci ta Sahara ( Transharan Trade Centre route). Wannan dalilin yasa har lokacin da aka kafa Nigeria, Katsina tana daya daga cikin Santoci na Layin Dogo ( Railway) a lokacin.
An bude Katsina College a lokacin mulkin Sarkin Katsina Muhammadu Dikko( 1906-1944). Tarihi ya nuna cewa Sarkin Katsina Muhammadu Dikko shine bayar da Filin da aka Gina Makarantar acikin gonar shi dake Rafukka, wadda ake cema Kofa 3 yanzu. An kammala ginin Makarantar a cikin shekarar 1921 aka bude ta a shekarar 1922. Makarantar a lokacin ta Kasance wata babbar Jamia ce ta mutanen Arewa, domin daga kowane lardi na Arewacin Nigeria akwai daliban da suka halarci Kwalejin Katsina don neman ilimi, kusan ace, wannan Kwalejin ta Katsina itace ta fara fitar da shuwagabannin Arewa na Jamhuriya ta farko. Kadan daga cikin daliban Katsina College sune:-. 1. Sir Ahamadu Bello , Sardauna Sokoto Kuma shine Firimiyan Jahar Arewa na Farko, Yana daya daga cikin daliban Katsina College, 2. Sir Abubakar Tafawa Balewa, Priminister Nigeria a Jamhuriya ta daya, 3. Alhaji Musa Yar'adua , Minister for Lagos Affairs, a Jamhuriya ta daya, 4. Alhaji Isah Kaita Wazirin Katsina, Minister jamhiriya ta daya, 5. Alhaji Sir Usman Nagogo Sarkin Katsina/ Minister without portpolio. 6. Sir Kashim Ibrahim Wazirin Borno, 7. Malam Saadu Zungur, founder of Nepu and first Northerner to attend Yaba High College Lagos, 8. Alhaji Abubakar Imam, first Editor Gaskiya tafi Kwabo, and autho of so many books including Ruwan Bagaja, Magana Jari da sauransu. 9. Malam Bukar Dafcharima, Minister first Republic. 10. Alhaji Nuhu Bamalli, Regional Minister, 11. Alhaji Muhammad Bashar Minister and later Sarkin Daura, 12. Malam Usman Iya-Iyai, Mathematics Teacher Katsina Middle School, 13. Alhaji Iro Yamel, a teacher at Katsina Middle School da sauransu.
Kadan kenan daga cikin daliban da Katsina College ta yaye.
Alhaji Musa Gambo Kofar soro.