TUTOCIN SHEHU A KATSINA.
- Katsina City News
- 10 Jul, 2024
- 545
Tutocin Shehu a Katsina sun Samo asaline a lokacin da Mujaddadi Shehu Usman yayi Kira da a kaddamar da Jihadin Musulunci a Kasar Hausa. Mutum na farko da Shehu Mujaddadi ya fara ba Tutar Musulunci shine SA'I Mai Tuta. Sa'i Mai Tuta ya dade tare da Mujaddadi Shehu Usman Danfodio tun farkon Kiran Shehu a Degel. Shine mutum na farko daya fara rike Tutar musulunci a Yakin Tabkin Kwatto, Wanda aka Kara a ranar 21 ga watan February, 1804. Zuruar Sai Mai Tuta sunci gaba da rike babbar Tutar Daular Usmaniyya har lokacin da Turawan mulkin Mallaka suka ci Sokoto da Yaki a shekarar 1903 a Burmi ( Battle of Burmi) a wajen wannan yakinne Turawan Ingila suka tafi da Tutar Musulunci ta Daular Sokoto a Ingila, Basu dawo da wannan Tutar ba, har Sai daren da zaa ba Nigeria yancin Kai a shekarar 1959, suka damka ma Sardaunan Sokoto Kuma Premier Nigeria ta Arewa watau Sir Ahmadu Bello wannan Tutar shi Kuma Sardauna ya damka ta ga Sarkin Musulmi Abubakar III, shi Sarkin Musulmi ya damka ma zuruar Sai Mai Tuta wannan Tutar.
Game da Tutocin Katsina. A Katsina Mujahidai 3 sukayi takakkiya har Sokoto wajen Mujaddadi Shehu Usman Danfodio domin su amso tutar kaddamar da Jihadi da Kuma Jaddada addinin musulunci. Hogben S. J da Kirk Greene sun rubuta acikin littafinsu Mai suna The Emirate in Northern Nigeria cewa, lokacin da Malam Ummarun Dallaje da Na Alhaji da Malam Ummarun Dunyawa suka Isa wajen Shehu Usman Danfodio, Shehu yaba Kowane daga cikin su Kanana Tutoci, Sai yace su biya wajen Dansa Muhammadu Bello suyi Mashi ban kwana. Lokacin da suka Isa Gidan Sultan Muhammadu Bello Sai suka ishe bai fitoba, suka jira Bai fito, ba to sai Shi Malam Na Alhaji da Ummarun Dunyawa suka ce Ummarun Dallaje ya tsaya yayi masu ban kwana su zasu wuce Katsina. Lokacin da Muhammadu Bello ya fito Sai tarar da Ummarun Dallaje shi kadai ya tambayi sauran yace sunyi gaba sunce ayi masu ban kwana, to sai Muhammadu ya sake bashi babbar Tuta Kuma yace shine zai zama Sarkin Katsina idan an kare Jihadi. Wannan shine dalilan da yasa aka samu Tutocin Shehu guda (3) a Katsina.
Har ya zuwa yanzu idan anzo Taron Sallah a Katsina zaka iske Sarkin Tuta a gaban Tawagar Sarki dauke da sample na Tutar da Muhammadu Bello Yana Ummarun Dallaje.
Musa Gambo Kofar soro.