Tsadar Rayuwa: Tinubu Ya Rufe Kofofinsa, Har Wasu Ministoci Ba Sa Samunsa – Ndume
- Katsina City News
- 10 Jul, 2024
- 475
Daga Zaharaddeen Ishaq Abubakar
Mai Tsawatarwa na Majalisar Dattijai, Ali Ndume, ya bayyana damuwa kan hauhawar farashin kayan abinci da rashin wadatar abinci.
A wata hira da ya yi da BBC Hausa, Ndume ya ce gazawar gwamnatin tarayya wajen magance wadannan matsalolin babban kalubale ne, yana mai cewa wasu ministoci ba sa iya ganin Shugaba Bola Tinubu domin tattauna batun.
Ya ce: “Babban matsalar wannan gwamnati ita ce ta rufe kofofinta, har wasu ministoci ba sa iya ganin Shugaban kasa, balle kuma ‘yan Majalisar Tarayya da ba su da damar ganawa da shi domin tattauna matsalolin da ke addabar mazabunsu.”
Ya yi wannan jawabi ne jim kadan bayan shi da abokin aikinsa, Sanata Sunday Steve Karimi, sun gabatar da kudiri domin magance matsalar karancin abinci a kasar.
Sun lura cewa Hukumar Abinci ta Duniya ta gargadi cewa mutum miliyan 82 na Najeriya na iya fuskantar rashin wadatar abinci cikin shekaru biyar masu zuwa.
Sanatan ya ce manufar kudirin ita ce jawo hankalin gwamnati kan tsananin matsalar karancin abinci da ke addabar ‘yan Najeriya da dama.
Ya nuna damuwa cewa idan gwamnati ba ta dauki matakin gaggawa ba, lamarin na iya jawo yunwa da fatara musamman ga yara.
“Muna so mu jawo hankalin gwamnati cewa Najeriya ba kawai tana fama da tsadar rayuwa ba, har ma da rashin wadatar abinci.”
“Muna so Shugaban kasa ya shiga tsakani kan matsalar tsadar rayuwa da karancin abinci”, in ji shi.
Ya bayar da misali da Jihar Katsina, inda yara ke fama da rashin gina jiki sakamakon karancin abinci.
Ya kuma ambaci halin da ake ciki a Jamhuriyar Nijar da Sudan ta Kudu, inda yara ke mutuwa sakamakon yunwa.
“Muna ganin yadda lamarin ya faru a Jamhuriyar Nijar da Sudan ta Kudu, inda yara ke mutuwa sakamakon yunwa, kuma muna fara ganin hakan a Najeriya”, in ji Sanata Ndume.
Yayin da ya ke kira ga gwamnati da ta dauki matakin gaggawa domin magance matsalar karancin abinci, ciki har da ganawa da kwararru da sauran masu ruwa da tsaki domin nemo mafita, ya nuna rashin jin dadinsa kan yadda gwamnati ba ta dauki wani kwakkwaran mataki ba duk da alkawuran da ta yi.
“Abin da muke so gwamnati ta yi shi ne ta zauna da kwararru da sauran masu ruwa da tsaki domin nemo mafita ga wannan matsalar. Muna kira ga gwamnati da ta dauki mataki, kada su manta cewa Najeriya na fama da tsadar rayuwa da kuma matsanancin karancin abinci.”
“Muna tsoron cewa wata rana na iya zuwa inda ko da mutum na da kudin siyan abinci, za su je kasuwa ba su samu ba” in ji shi.