Wani Uba ya Yanke Alaƙa Ta Jini Tsakaninsa Da Ɗansa akan Miyagun Ɗabi'u.

top-news

Zaharaddeen Ishaq Abubakar, Katsina Times 

A wata sanarwa da aka wallafa a jaridar Daily Trust ta ranar Talata, 9 ga watan Yuli, Abdulmumini Yunusa, mazaunin Asokoro, Abuja, ya bayyana matsayinsa kan ɗansa, Mohammed Dahiru Abdulmumini.

Abdulmumini Yunusa ya bayyana cewa ya haifi, ya reni, kuma ya kula da Mohammed tun daga haihuwarsa har zuwa yau. Duk da haka, ya ce ɗansa ya zame masa tamkar ƙaya a cikin Maƙoshi saboda miyagun halaye da ɗabi'u marasa kyau da suka haifar masa da matsaloli iri-iri. Ya ce duk ƙoƙarinsa na gyara ɗansa sun ci tura.

Sanarwar ta bayyana cewa Abdulmumini Yunusa ya yanke duk wata alaka da ɗansa, ciki har da ta jini, zamantakewa, da kasuwanci. Ya ƙara da cewa Mohammed Dahiru Abdulmumini ba zai sami damar amfani da duk wata kadara da ya gada daga gare shi ba, banda gida mai ɗaki biyu da yake ciki a Abuja.

Yunusa ya bayyana cewa ya ɗauki wannan mataki ne domin kare martabarsa da kasuwancinsa, kuma ya nemi jama'a su yi hattara da duk wata mu'amala da ɗansa.

Sanarwar ta ƙare da cewa, Abdulmumini Yunusa ya shaida wannan hukunci bisa ga dokar rantsuwa ta shekarar 2004.

NNPC Advert